Matasan Arewa Sun Fadi Sunayen 'Yan Siyasa 3 da Ke Shirin Ruguza Gwamnatin Tinubu
- Wata kungiyar kawo sauyi ta matasan Arewa ta zargi wasu 'yan siyasar Najeriya uku da yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu
- Shugaban kungiyar, Bilal Abdulahi, ya yi kira ga hukumomin tsaro su binciki wannan yunkuri tare da daukar matakan dakile su
- Kungiyar ta bukaci matasa da 'yan kasa su goyi bayan Tinubu tare da yin watsi da shirin su Rotimi Amaechi da zai haifar da rikici
- Wannan ra'ayin RAYCN ne kuma kungiyar ba ta iya gabatar da hujjojin da za su tabbatar da zargin da ta ke yi wa wadannan mutane ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata kungiyar matasan Arewa (RAYCN) ta zargi wasu manyan 'yan siyasar Najeriya da yunkurin wargaza gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar RAYCN ta lissafa sunayen 'yan siyasar da suka hada da: Rotimi Amaechi, Attahiru Bafarawa, da Sani Abdullahi Shinkafi.

Kara karanta wannan
Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya

Asali: Twitter
Ana zargin su Amaechi da yunkurin ruguza Tinubu
RAYCN ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Alhamis, inda ta ce 'yan siyasar uku ba sa son ci gaban Tinubu, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan sun yi ikirarin cewa shirin 'yan siyasar ya haɗa da tara matasa da shirya zanga-zanga a yankin Arewa maso Yamma, daga Bafarawa zuwa Sokoto da Zamfara.
Shugaban kungiyar, Bilal Abdulahi, ya ce Amaechi na bayar da kudi ga Bafarawa, wanda kuma ke amfani da su wajen ɗora Shinkafi don yaƙar gwamnatin Tinubu.
Kungiyar matasan RAYCN ta fadi zargin da take yi
Bilal Abdulahi ya bayyana cewa:
"Manufarsu ita ce tsoratar da gwamnati da kuma nuna wa ‘yan Najeriya cewa ba a daukar matakan inganta rayuwarsu.
"Al’amarin ya zama barazana ga tsaron kasa. Wannan shiri na iya durkusar da Najeriya idan ba a dauki matakin gaggawa ba."

Kara karanta wannan
'Za mu dauki mataki': Abin da Sanusi II ya ce da aka kashe mutane wajen rusau Kano
Ba tare da kawo wasu hujjoji ba, kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro su binciki batun tare da daukar matakin gaggawa domin dakile wannan zargi.
An caccaki shirin Amaechi, Bafarawa da Shinkafi
Kungiyar ta kuma yi kira ga matasa, kungiyoyin addini, da masu son zaman lafiya su goyi bayan gwamnatin Tinubu wajen gyara Najeriya.
A wani bidiyo da PRN ta wallafa a shafinta na X, ya rahoto Bilal Abdulahi ya na cewa:
"Wannan yunkuri na nuna kokarin kifar da gwamnati ta hanyar da ta sabawa doka, kuma lallai dole ne a dakatar da su."
Ya kara da cewa tun bayan faduwarsu a zabe, Amaechi, Bafarawa, da Shinkafi suka kasa boye kiyayyarsu ga Tinubu da gwamnatinsa.
"Abin takaici ne cewa wannan kiyayyar ta kai su ga aikata abin da zai zama barazana ga dimokradiyya da doka a kasar."
- Bilal Abdullahi.
Kalli bidiyon a kasa:
Bafarawa ya fice daga jam'iyyar PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
A cikin wasikar da ya fitar, Bafarawa ya ce lokaci ya yi da zai bude sabon babi a rayuwarsa, lamarin da ake ganin zai kara hargitsa PDP.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng