"Gwamnati Ta Yi Banza da Mu," ASUU Ta ce ba a Damu da Barazanar Yajin Aikinta ba

"Gwamnati Ta Yi Banza da Mu," ASUU Ta ce ba a Damu da Barazanar Yajin Aikinta ba

  • ASUU ta ce har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta dauki wani mataki mai ma'ana don cika alkawuran da aka yi ba.
  • Kungiyar na ganin babu wata matsala da gwamnati ta warware gaba daya tun bayan hawanta mulki fiye da shekara guda.
  • ASUU za ta gana nan gaba kadan domin yanke shawarar matakin da za ta dauka kan lamarin tun da ba za a kula ta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana matukar takaicinta kan gazawar Gwamnatin Tarayya na cika kowanne daga cikin bukatunta.

Wannan na na zuwa ne duk da kungiyar ta amince a bi hanyar lumana wajen warware sabanin da suka dade suna fuskanta da gwamnatocin kasar nan.

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa hukumar tsaro mallakin Kano

Ilimi
ASUU na shirin sake zama bayan gwamnati ta yi watsi da ita Hoto: ASUU/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A labarin da ya kebanta da Nigerian Tribune, shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta dauki wani matakin da zai warware kokensu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya-bayan nan dai, ASUU ta ci gaba da barazanar tafiya yajin aiki a fadin kasar idan har gwamnati ta ci gaba da kin cika alkawuranta, amma hakan bai wani yi tasiri ba.

Gwamnati ta yi gum da bukatun ASUU

A cewar Osodeke, har yanzu gwamnati ba ta dauki wani mataki ba face kafa tawagar sake tattaunawa da ASUU kwanan nan domin sake duba koken kungiyar.

Kungiyar malaman ta bayyana cewa ta kammala nata bangaren na duba abubuwan da ake bukata, kuma ta na jiran amsar gwamnati zuwa yanzu.

ASUU ta mika wa wakilan gwamnati bukatunta

A cewar Farfesa Osodeke, ASUU ta gabatar da matsayarta kan kowane batu da ake tattaunawa a kai, inda ta bar wa wakilan gwamnati su koma su tattauna da manyansu sannan su dawo da sakamako domin a san matsayar kowa.

Kara karanta wannan

Tsanyawa/Kunchi: Mutanen Kano sun shafe shekara 1 babu 'dan majalisar dokokin jiha

Ya ce:

"Yanzu kusan watanni biyu kenan, amma har yanzu tawagar gwamnati ba ta dawo gare mu ba, balle ta rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya, kuma hakan na nufin cewa ‘yan siyasa ba su damu da ci gaban jami’o’in gwamnati ba."

ASUU ta zargi gwamnatin Tinubu da gazawa

A cewarsa, kafin wannan gwamnati, gwamnatocin da suka shude kan dauki wani mataki, koda kuwa bai taka kara ya karya ba, domin inganta bangaren ilimi, amma babu wani abu da wannan gwamnati ta yi kawo yanzu.

Shugaban ASUU ya ce:

"Ba a warware ko da matsala daya ba daga cikin matsalolin da suka shafi yarjejeniyarmu tun bayan shigowar wannan gwamnati fiye da shekara daya da ta gabata.
"Saboda haka, a fannin ilimi, muna da yakinin cewa babu wani canji. Har yanzu muna fuskantar matsalolin da muke fama da su tun da dadewa, alhali masu kudi na ci gaba da aika ‘ya’yansu kasashen waje domin karatu, suna dawowa su kama manyan mukamai, musamman a hukumomin gwamnati, yayin da ‘ya’yan talakawa ke ci gaba da shan wahala."

Kara karanta wannan

'Za mu iya': Tinubu ya dauki mataki da Amurka ta janye tallafin yaki da cutar HIV

Shugaban ya tabbatar da cewa ‘yan kungiyar ASUU za su gana nan ba da jimawa ba domin yanke shawarar mataki na gaba da za su dauka.

Gwamnatin Tinubu ta fusata ASUU

A baya, mun ruwaito cewa Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta nuna damuwa kan yadda gwamnati ke tafiyar da harkar ilimi, tana mai cewa wannan sakaci ne babba.

Shugaban ASUU reshen Jami'ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole, ya bayyana cewa wannan halin ko-in-kula ya na hana kwararrun malamai sha'awar koyarwa a makarantun gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.