Kotu Za Ta Yanke Hukunci kan Shari'ar Mabarata da Minista bayan Korafin Abba Hikima
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 18 ga Fabrairun 2025 don sauraron karar da wasu mabarata suka shigar kan kama su ba bisa ka’ida ba
- Lauyan masu kara, Usman Chamo, ya ce har yanzu ana ci gaba da takura wa masu karamin karfi, yana mai cewa Wike ya “ayyana yaki da bara” a Abuja
- Lauyan Hukumar DSS, A.K. Karobo-Tamuno, ya bukaci kotu ta yi watsi da karar, yana mai cewa ba ta da tushe ko wata madafa ta doka
- Wannan na zuwa ne bayan sanannen lauya a Kano, Abba Hikima ya shigar da korafi kan lamarin a madadin mabaratan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta shirya sauraran shari'a tsakanin yan bola jari da mabarata da kuma Nyesom Wike.

Kara karanta wannan
Tinubu ya ji takaicin konewar almajirai, ya ba da umarnin dakile gobara a tsangayu
Kotun ta sanya ranar 18 ga watan Fabrairun 2025 don sauraron karar da wasu da mabaratan suka shigar kan kama su ba bisa ka’ida ba.

Asali: Facebook
Korafin Abba Hikima kan Wike a Abuja
Alkalin kotun, James Omotosho, ya ba da umarnin aika takardun kotu ga Sufeto Janar na ’Yan Sanda, NSCDC, da Antoni Janar na Tarayya, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan karar an shigar da ita ne a madadin masu kananan sana'o'i da mabarata ta hannun lauya Abba Hikima, yana mai cewa kame su ba bisa doka ba haramun ne.
A cewarsa, hana marasa matsuguni da sana’ar tattara tarkace da kananan ’yan kasuwa, da masu bara ya saba ka’ida.
An bukaci watsi da korafin Abba Hikima
Tun da farko, lauya mai kare wadanda suka shigar da kara, Usman Chamo, ya shaidawa kotu cewa har yanzu ana ci gaba da takura musu a Abuja.

Kara karanta wannan
Tinubu ya gana da Aminu Ado Bayero, ya ba shi tabbacin kawo karshen matsaloli a Kano
Ya bayyana cewa Wike ya “ayyana yaki da bara” a yankin, lamarin da ya jawo kame da tsare wasu da ke sana’o’in neman abinci.
A martaninsa, lauya mai kare hukumar DSS, A.K. Karobo-Tamuno, ya shaidawa kotu cewa sun shigar da wata takarda don a yi watsi da karar.
A cewarsa, karar ba ta da tushe ko wata madafa ta doka, domin haka kotu ya kamata ta yi watsi da ita gaba daya.
Gwamna ya yi wa Wike wankin babban bargo
Kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya mayar da martani kan kalaman ministan birnin tarayya, Nyesom Wike.
Gwamnan ya yi kira ga Wike da ya rungumi gaskiya da da’a a siyasa maimakon ya rika nuna rashin kwarewa da rarraba kawuna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng