Gwamnatin Kano Ta Kashe Sama da N1.5bn a Gina Mayanka a Kananan Hukumomi
- Gwamnatin Kano za ta kaddamar da sababbin wuraren yanka dabbobi guda 20 da aka gina a kananan hukumomi daban-daban
- An gina kwatan ne domin tsabtace sarrafa nama, dakile cututtukan dabbobi, da kare lafiyar jama’a daga cututtuka masu yaduwa
- Gwamnati ta bukaci masu fawa da su rungumi dabarun zamani a fannin sarrafa nama don tabbatar da tsafta da inganci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano za ta kaddamar da sababbin kwata guda 20 da aka gina a fadin jihar, wanda aka kiyasta darajarsu ya kai N1,550,825,750.95.
An gina wadannan kwata ne karkashin shirin bunkasa noma da kiwo na jihar (KSADP), a yankuna daban-daban na kananan hukumomin da ke jihar.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa kananan hukumomin da suka amfana sun hada da Dawakin Tofa, Kunchi, Bichi, Gezawa, Tudun Wada, Kura, da Rano.

Kara karanta wannan
Tsanyawa/Kunchi: Mutanen Kano sun shafe shekara 1 babu 'dan majalisar dokokin jiha
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran kananan hukumomin sun hada da Bebeji, Wudil, Doguwa, Gabasawa, Gaya, Sumaila, Takai, Kabo, Shanono, Karaye, Kiru, da kuma Gwarzo.
Yadda aka gina sababbin mayanka a Kano
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Bankin Raya Kasashen Musulunci (IsDB), Lives and Livelihood Funds, da Gwamnatin Jihar Kano ne suka hadu wajen daukar nauyin aikin.
Da yake jawabi a taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Kano, Shugaban KSADP, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa aikin ya kammala kuma an shirya tsaf don kaddamar da shi.
Kano: Za a fara aiki a sababbin mayanka
Ibrahim Muhammad ya jaddada cewa wajibi ne a fara amfani da wadannan wurare nan take don hana su lalacewa ko fuskantar satar kayan aiki.
Ya ce:
“Manufar wannan shiri shi ne,a tabbatar da tsaftace nama, kula da cututtukan dabbobi, da dakile yaduwar cututtuka masu hadari ga lafiyar jama’a.”
Sarkin fawa ya yabi Gwamnatin Kano
Da yake nuna godiyarsa ga gwamnati da masu daukar nauyin aikin, Sarkin Fawar Kano, Alhaji Isyaku Muri, ya bayyana shirin a matsayin gagarumin ci gaba a fannin sarrafa nama a zamanance.
Haka nan, Shugaban Hukumar Raya Noma da Karkara ta Kano (KNARDA), Dr. Farouk Kurawa, ya bukaci masu sana’ar fawa da su rungumi dabarun zamani wajen sarrafa nama.
Za a kafa hukumar tsaro a Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa Majalisar dokokin jihar har Kano ta amince da kudirin da ya ba Gwamna Abba Kabir Yusuf damar kafa sabuwar Hukumar Tsaro mallakin jihar.
Majalisar ta ce wannan mataki ya biyo bayan nazari mai zurfi da majalisar ta yi kan kudirin, tare da gindaya sharudda don tabbatar da cewa hukumar za ta yi aiki ba tare da siyasa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng