'Na Bambanta da Su': Buhari Ya Fadi Halin da Abokansa na Yarinta da Karatu Ke Ciki
- Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ce da yawa daga cikin abokan karatunsa sun riga mu gidan gaskiya a yau
- Buhari ya ce ya godewa Allah SWT da rayuwarsa inda ya ce da yawa daga cikinsu suna fama da matsaloli da larurar lafiya
- Tsohon shugaban ya bayyana cewa rayuwar soja ta taimaka masa wajen kula da lafiyarsa, kuma har yanzu yana da ƙwarin jiki
- Hakan ya biyo bayan bugan kirji cewa mulkinsa ya maida hankali kan tsaro da tattalin arziki, kuma ya yi iya bakin ƙoƙarinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Katsina - Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce ko da yake yana raye kuma yana da ƙoshin lafiya, da yawa daga cikin abokan karatunsa sun rasu.
Muhammadu Buhari ya kuma ce wasu daga cikin abokan karatunsa da ke raye, suna samun taimakon 'yan uwansu game da matsalolin lafiya da suke fama da su.

Kara karanta wannan
'Na yi kokari': Buhari ya jero bangarorin da ya kawo sauyi a mulkinsa, an yaba masa

Source: Twitter
Koshin lafiya: Buhari ya yi godiya ga Allah
Tsohon shugaban ya faɗi haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu 'yan jarida a gidansa da ke garin Daura, Jihar Katsina, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya ce yana godiya ga Allah da yake iya tafiya yana yin ayyuka na yau da kullum, ciki har da karɓar baƙi a gidansa ranakun Juma’a da Lahadi.
Ya ce yana tunanin lafiyarsa ta jiki da ta kwakwalwa na da alaƙa da rayuwar soja, wanda ya taimaka masa wajen kula da kansa da samun ƙoshin lafiya.
Yadda mutane ke yabon koshin lafiyar Buhari
Buhari ya ƙara da cewa mutanen da ke ganinsa suna cewa yana da ƙoshin lafiya fiye da lokacin da yake shugabanci kuma har yanzu yana iya aikinsa na yau da kullum.
Buhari har ila yau, ta yi magana kan yadda ya gudanar da mulkinsa a Najeriya da nasarorin da ya samu.
Ya ce shugabantar Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, amma duk da haka, an samu wasu manyan nasarori a tsawon shekaru takwas na mulkinsa.
Buhari ya magantu kan fentin gidansa a Kaduna
Buhari ya kuma bayyana cewa ya gina gidansa na Daura kafin ya shugabanci asusun PTF, kuma gidan da ke Kaduna bai da fenti na tsawon shekaru.
Sai dai ya ce gwamnatin tarayya ce ta taimaka wajen fentin gidan nasa na Kaduna, cewar jaridar ThisDay.
Dattijon ya jinjinawa 'yan jarida saboda irin rahotannin da suka yada musamman a lokacin mulkinsa.
Tsohon hadimin Buhari ya magantu kan cin hanci
Kun ji cewa tsohon mai ba da shawara ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci a aiwatar da hukuncin kisa ga masu cin hanci da rashawa a Najeriya.
Okon Obono Obla ya ce wannan mataki mai tsauri zai hana mutane aikata rashawa, wanda ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewa tsakanin al'umma.
Obla ya jaddada bukatar inganta hukumomi, inganta gaskiya da rikon amana, tare da hukunta masu aikata laifuffukan rashawa don inganta kasa baki daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
