Majalisa Ta Amince Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kafa Hukumar Tsaro Mallakin Kano

Majalisa Ta Amince Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kafa Hukumar Tsaro Mallakin Kano

  • Majalisar Kano ta hana duk wani dan siyasa shugabantar hukumar tsaro don tabbatar da aiki ba tare da katsalandan na siyasa ba
  • Sabuwar dokar ta bai wa jami’an hukumar ikon daukar makamai, kama masu laifi, da mika su ga ‘yan sanda domin gurfanarwa
  • Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Hussaini Dala ya fadi tsarin da za a bi wajen daukar shugaban hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kudirin dokar da zai ba gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ikon kafa sabuwar hukumar tsaro.

Amincewar ta biyo bayan tattauna wa mai zurfi kan muhimman sassan kudirin, ciki har da sashen da ya haramta bai wa dan siyasa jagorancin hukumar.

Kara karanta wannan

Tsanyawa/Kunchi: Mutanen Kano sun shafe shekara 1 babu 'dan majalisar dokokin jiha

Gwamna
Za a kafa sabuwar hukumar tsaro a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban masu rinjaye, Hon. Lawan Husaini Dala, ya bayyana cewa majalisar ta yi cikakken nazari kan kudirin don tabbatar da cewa dokar za ta amfanar da jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin majalisa na amince wa da kirkirar hukumar

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa bayan amincewar da aka yi da kudirin, Hon. Lawan Husaini, ya bayyana cewa an bi dukkan ka’idojin dokoki kafin majalisa ta amince da shi.

Dan majalisar ya bayyana cewa hukumar tsaron za ta kasance wani bangare na tsaron al’umma, wanda zai taimaka wajen karfafa aikin hukumomin tsaro a jihar.

Ya jaddada cewa kirkirar sabuwar hukumar za ta inganta tsaro a Kano, inda ya yi nuni da irin matakin da jihohin Kudu suka dauka na kafa hukumomin tsaro kamar Amotekun domin karfafa tsaro a yankunansu.

Hon. Husaini ya bayyana cewa hukumar za ta samu cikakken ikon rike makamai bisa doka, tare da ikon kama masu laifi da mika su ga ‘yan sanda domin gurfanarwa a kotu.

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Majalisa: Sharuddan daukar ma’aikatan hukumar tsaro

Shugaban masu rinjaye na majalisar ya kuma bayyana cewa duk wanda za a dauka aiki a hukumar ba zai kasance 'dan kowace jam’iyyar siyasa ba.

Hon. Dala ya ce:

“A cewar dokar, shugabancin hukumar zai kasance a hannun wani dan asalin jihar Kano wanda ba shi da wata alaka da kowace jam’iyyar siyasa."

Majalisa ta fadi sharadin zabar shugaban hukumar tsaro

Hon. Lawan Husaini Dala ya kara da cewa za a nada Kwamanda Janar na hukumar, wanda dole ne ya zama mutumin kirki mai kima da kwazo, sannan kowace karamar hukuma za ta nada kwamanda.

Ya ce dole Kwamanda Janar din ya zama tsohon jami’in soja ko ‘yan sanda da ya shafe akalla shekaru 25 yana aiki, kuma ba zai kasance a ƙasa da mukamin Kanal a soja ko Kwamishinan ‘yan sanda ba.

Hon. Dala ya kara da cewa hukumar tsaron za ta samu kwamitin gudanarwa da za a dora wa alhakin tafiyar da ita, tare da shugaban da gwamna zai nada.

Kara karanta wannan

Bayan shawarar gwamnoni, majalisa za ta zauna domin tabbatar da kudirin haraji da gaggawa

Majalisar Kano ta fadi amfanin kafa hukumar tsaro

A baya, mun ruwaito cewa, Majalisar dokokin Kano ta bayyana cewa samar da hukumar tsaro mallakin jiha zai taimaka wajen magance matsalolin daba, kwacen waya da makamantansu.

Majalisar ta ce za ta ba gwamna, Abba Kabir Yusuf ikon ya samar da hukumar, kuma tuni aka fitar da tsarin da za a bi wajen gudanar da ita da kuma hanyar zabar wanda zai shugabance.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.