Tinubu Ya ba Sakataren APC a Kano Babban Muƙami bayan Minista Ya bar Kujerar

Tinubu Ya ba Sakataren APC a Kano Babban Muƙami bayan Minista Ya bar Kujerar

  • Sakataren jam'iyar APC a Kano, Alhaji Ibrahim Zakari Sarina ya zama sabon kwamishinan Hukumar Koke-Koke (PCC) mai wakiltar jihar
  • Nadin Sarina shi yake tabbatar da shi a matsayin wanda ya maye gurbin karamin Ministan raya gidaje na kasa, Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata
  • Ata ya rike mukamin kwamishinan PCC daga Yuli zuwa Oktobar 2024 kafin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi a matsayin minista
  • Shugaban Majalisar Dattawa watau Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da nadin Sarina a yayin zaman majalisa na yau Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Zakari Sarina ya samu muƙami a gwamnatin Bola Tinubu.

Tinubu ya amince da nadin Sarina a matsayin kwamishinan Hukumar Koke-Koke (PCC), mai wakiltar jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Waye sakataren PDP?" Barau Jibrin ya zaƙalƙale da hatsaniya ta ɓarke a Majalisar Dattawa

Tinubu ya nada sakataren APC a Kano mukami
Bola Tinubu ya maye gurbin mukamin da minista ya rike a Kano inda ya nada sakataren APC. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Sarina ya sha alwashin kwace mulki daga NNPP

Sarina ya maye gurbin Hon. Yusuf Abdullahi Ata, wanda yanzu haka shi ne Karamin Ministan Harkokin Gidaje da Raya Birane na Tarayya, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan nadin na Sarina na zuwa ne watanni biyu bayan ya bugi kirji cewa jam'iyyar APC mai adawa a jihar za ta kwace mulki daga wajen NNPP.

Hakan bai rasa nasaba da sauya sheka da 'ya'yan jam'iyyar NNPP sama da 2,000 suka yi a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu zuwa jam'iyyar APC a hukumance.

Sakataren APC a Kano, Malam Ibrahim Zakari Sarina ya ce wannan alama ce da ke nuna jam'iyyar za ta ƙwace mulkin Kano a zaɓen shekarar 2025.

An nada Sarina kwamishina a hukumar PCC

Kafin nadin Sarina, Ata ya rike mukamin kwamishinan PCC mai wakiltar Kano daga Yuli zuwa Oktobar 2024 kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya naɗa shi minista, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da Aminu Ado Bayero, ya ba shi tabbacin kawo karshen matsaloli a Kano

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Obot Akpabio, GCON, ne ya bayyana nadin Sarina a yayin zaman majalisar da aka yi a yau Laraba 5 ga watan Janairun 2025.

Tinubu zai kori kwamishinonin zaben jihohi 3

Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa don korar kwamishinonin INEC guda uku da aka dakatar a Najeriya.

Kwamishinonin da ake so a kora sun hada da Ike Uzochukwu daga jihar Abia da Hudu Yunusa-Ari daga Adamawa da Nura Ali daga Sokoto saboda zargin rashin da’a.

A cikin wasikarsa, Tinubu ya bayyana cewa an dakatar da kwamishinonin tun kafin ya hau mulki, don haka yana neman a kore su gaba daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.