Tinubu Ya Bukaci Korar Kwamishinonin Zabe a Jihohi 3 kan Zargin Rashin Da'a a 2023
- Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa don korar kwamishinonin INEC guda uku da aka dakatar a Najeriya
- Kwamishinonin da ake so a kora sun hada da Ike Uzochukwu (Abia), Hudu Yunusa-Ari (Adamawa), da Nura Ali (Sokoto), saboda zargin rashin da’a
- A cikin wasikarsa, Tinubu ya bayyana cewa an dakatar da kwamishinonin tun kafin ya hau mulki, don haka yana neman a kore su gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin korar Kwamishinonin zabe na jihohi (RECs) da aka dakatar.
Bukatar shugaba Bola Tinubu tana cikin wata wasika da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Asali: Facebook
An ba da belin Hudu kan zargin rashin da'a

Kara karanta wannan
"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala
Kwamishinonin da Tinubu ke son a kora su ne Ike Uzochukwu (Abia), Hudu Yunusa-Ari (Adamawa), da Nura Ali (Sokoto), wadanda ake zargi da rashin da’a, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan ba da belin dakataccen kwamishinan zaɓe na hukumar INEC a jihar Adamawa, Farfesa Hudu Yunusa-Ari.
Hudu da shi da sauran wasu jami'ai da ke amsa tambayoyi a hannun ƴan sanda ne dai aka ba da belin su a watan Mayun 2023.
Kwamishinan yana fusƙantar tuhuma ne kan zargin karɓar cin hanci lokacin zaɓen cike gurbin gwamnan jihar Adamawa.
Ana zargin su da aikata ba daidai ba da rashin da'a a lokacin babban zaben 2023 da aka gudanar a Najeriya.
Tinubu ya bukaci korar kwamishinonin zabe 3
Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, ya karanta wasikar a zauren majalisa yayin zaman da aka yi a ranar Laraba 5 ga watan Janairun 2025.
A cikin wasikar, Tinubu ya bayyana cewa INEC ta dakatar da kwamishinonin tun kafin ya hau mulki fiye da shekara guda da ta wuce, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
'Ba su kai 900 ba': Kaduna Electric ya fadi adadin ma'aikatan da ya kora daga aiki
“Majalisar Dattawa ta lura cewa an dakatar da kwamishinonin tun watan Maris 2022, kafin wannan gwamnati ta hau mulki.”
“Ina da yakinin cewa Majalisar Dattawa za ta duba wannan bukata da gaggawa, Ina gode muku.”
- Cewar sanarwar
Tinubu ya nemi a kara kasafin kudin 2025
Kun ji cewa Bola Tinubu ya bukaci a kara kasafin kudin 2025 daga N49.7trn zuwa N54.2trn, bisa karin kudin shiga da gwamnati ta samu daga wasu hukumomi.
Wasikar Shugaban kasa zuwa Majalisar Dattawa ta ce FIRS ta samu N1.4trn, Kwastam ta samu N1.2trn kuma sauran hukumomi sun tara N1.8trn.
Bayan karanta wasikar, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya tura bukatar ga Kwamitin Kasafin Kudi don nazari kafin karshen Fabrairun 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng