"Ba Za Mu Bari ba," Lauya, Abba Hikima Ya Je Inda Ake Harbe Mutane wajen Rusau a Kano

"Ba Za Mu Bari ba," Lauya, Abba Hikima Ya Je Inda Ake Harbe Mutane wajen Rusau a Kano

  • Fitaccen lauya, Abba Hikima, ya bayyana damuwarsa kan yadda jami’an tsaro suka gudanar da rusau a Rimin Zakara, wanda ya kashe mutane
  • Ya zargi jami’ar Bayero da sakaci, yana mai cewa sun bar jama’a su gina gidaje sama da 10, 000 a wurin ba tare da an sanar da su rikicin filin ba
  • Baristan ya bukaci gwamnatin Abba Kabir Yusuf da ta gudanar da bincike mai zurfi kan yadda aka rasa rayuka a rushe-rushen don daukar mataki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Daya daga cikin lauyoyin da ke fafutukar kare hakkin dan Adam, Abba Hikima ya bayyana takaicin halin da jami’an tsaro su ka jefa jama’ar Rimin Zakara.

Rusau da aka yi a daren Lahadi ya yi sanadiyyar rasuwa mutane hudu a cikin dare, yayin da jama’a su ka riga sun fara bacci.

Kara karanta wannan

Tsanyawa/Kunchi: Mutanen Kano sun shafe shekara 1 babu 'dan majalisar dokokin jiha

Hikima
Abba Hikima ya fadi yadda ya tarar da mazauna Rimin Zakara Hoto: Abba Hikima
Asali: Facebook

Ya tabbatar wa Legit cewa wasu daga cikin jami’an da aka ce an kai wajen rusau din har da jami’ai dauke da adduna da sauran makamai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Hikima ta sakon ta sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, da cewa ya samu jama’ar Rimin Zakara a cikin mawuyacin hali, yayin da ake ci gaba da da zaman makoki.

"An illata mazauna Rimin Zakara," Abba Hikima

A tattaunawarsa da Legit ta wayar tarho, Abba Hikima ya bayyana cewa ya ziyarci Rimin Zakara, inda aka kashe mutum hudu da illata wasu da dama.

A kalamansa, mutanen garin sun ga jami'ar da motoci, dauke da adduna da sauran miyagun makamai da su ka hada da bindigu domin yin rusau.

Ya ce:

"Na ga gurin zaman makoki na mutanen da su ka rasu, na kuma ga mutanen da aka ji wa ciwo, da ciwon harbi. Sannan kuma na ga gidaje da shaguna wanda aka ruguje.

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Wannan abin lallai ba daidai ba ne ba, ya saba wa kowace irin doka, ya kuma saba wa tsari na waye wa, musamman a ce a cikin dimukuradiyya ake yin wannan.

Abba Hikima ya caccaki mahukuntan BUK

Fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya bayyana cewa ko da jama'ar Rimin Zakara 'yan kama wuri zaune ne, jami'ar Bayero ta yi sakaci har jama'a su ka yi gini sama da dubu goma a wurin.

Ya ce a rahoton da ya samu, mutane da dama ba su da masaniyar akwai rikici a kan filin kafin su sa kudinsu su saya.

Hikima ya ce:

"Kuma ita BUK ta na ina har ta bari aka zo aka gina wadannan gidajen. Akwai gidaje sun fi 10,000 a wannan wurin, na je jiya na gani, tafiya ce mai nisan gaske.

Abba Hikima ya nemi gwamnati ta yi bincike

Barista Hikima ya shawarci gwamnatin Abba Kabir Yusuf a kan ya tabbata an gudanar da sahihin bincike a kan yadda aka salwantar da rayukan jama'a.

Kara karanta wannan

An kama 'yan bindigar da suka ba basarake kudi domin kafa sansanin ta'addanci

Ya ce:

"Hukuncin da aka dauka a kansu ya yi nauyi, rai shi ne mafi girman abin da doka ta kare wa mutum. Lallai a bi hakkin mutanen nan na ransu.

Abba Hikima ya yi gargadin cewa matukar gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba, zai jagoranci nema wa mutanen nan hakkinsu a dokar Najeriya.

Rusau ya fusata majalisar dokokin Kano

A baya, kun ji cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano ta nuna damuwa kan rushe-rushe da aka yi a Rimin Zakara da tsakar dare, wanda ya haddasa mutuwar mutane hudu da raunata wasu da dama.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungogo, Hon. Aminu Sa'adu Ungogo, ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yana mai jaddada cewa ya kamata a dauki mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.