Shugaba Tinubu Zai Shilla zuwa Kasar Waje, Zai Ziyarci Kasashe 2
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairun 2025 domin zuwa ƙasar waje
- Mai girma Bola Tinubu zai shilla zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa domin yin wata ziyara ta ƙashin kansa
- Daga Paris, shugaba Tinubu zai zarce zuwa birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha a mako mai zuwa domin halartar wani taro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tafi zuwa birnin Paris, babban birnin ƙasar Faransa.
Shugaba Tinubu zai shilla zuwa birnin Paris ne domin wata “ziyara ta ƙashin kansa”, a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairun 2025.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Tinubu shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar wacce Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu zai halarci taro a Habasha
Bayo Onanuga ya bayyana cewa daga Faransa, shugaba Tinubu zai wuce zuwa birnin Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha, domin halartar taron ƙungiyar tarayyar Afirika (AU).
"A birnin Addis Ababa, shugaba Tinubu zai haɗu da sauran shugabannin Afirka a taro na 46 na majalisar zartarwa da kuma taro na 38 na shugabannin tarayyar Afirika, wanda aka shirya daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairu, 2025."
"Shugaban ƙasan zai isa birnin Addis Ababa a farkon mako mai zuwa domin halartar taron ƙungiyar tarayyar Afirika."
"Yayin da yake a Faransa, Shugaba Tinubu zai gana da takwaransa na Faransa, Shugaba Emmanuel Macron."
- Bayo Onanuga
Ana yawan surutu kan tafiye-tafiyen Tinubu
Tafiye-tafiyen Tinubu dai zuwa ƙasashen waje na yawan janyo suka daga jama’a, musamman ganin halin ƙuncin tattalin arziƙi da ƙasar ke ciki, inda ƴan Najeriya ke bayyana damuwarsu kan yawan mutanen da ke binsa.
Haka kuma, ana ci gaba da muhawara kan ko irin waɗannan tafiye-tafiye suna samar da fa’ida ga Najeriya, musamman dangane da jawo masu zuba hannun jari ƴan ƙasashen waje da habaka tattalin arziƙi.
Jaridar Daily Trust ta ce tun bayan hawan shugaba Tinubu mulki a watan Mayun 2023, ya ziyarci ƙasashe 19 a tafiye-tafiye 32 da ya yi.
Tinubu ya amince da aikin N80bn a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta amince a gyara madatsar ruwa ta Alau da ke jihar Borno.
Gwamnatin ta amince da N80bn domin gyara madatsar ruwan wacce ɓallewarta, ta haddasa mummunar ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
