Tsanyawa/Kunchi: Mutanen Kano Sun Shafe Shekara 1 babu 'Dan Majalisar Dokokin Jiha
- Mazabar Tsanyawa/Kunchi na ci gaba da zama ba tare da zababben wakili a Majalisar Dokokin Jihar Kano ba
- Masana siyasa da jama’a sun soki INEC da ‘yan siyasa kan gaza kammala zaben cikin wa’adin kwanaki 90 da kotu ta bayar
- Jama’ar yankin sun bukaci gwamnatin jihar da INEC su dauki mataki cikin gaggawa domin su ma su samu wakilci a majalisa
- Sun koka a kan yadda aka bar su a baya wajen samar da kayan more rayuwa a yankin da su ka ce ya na fama da koma baya sosai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Shekara guda kenan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da zaben cike gurbi a mazabar Tsanyawa/Kunchi.
Wannan na nufin har yanzu, yankin bai samu zababben wakili a Majalisar Dokokin Jihar Kano ba.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa INEC ta dakatar da zaben a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2024 bayan da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka tarwatsa tsarin kada kuri’a a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dakatar da zaben bayan dan takarar jam’iyyar NNPP, Yusuf Ali Maigado, ya shigar da kara, inda kotu ta umarci a gudanar da zabe cikin kwanaki 90.
An soki jinkirin INEC kan zaben cike gurbi
Trust radio ta wallafa cewa yayin da ake ci gaba da rashin wakilci a mazabar, wani masanin siyasa, Dr. Kabiru Sufi, ya ce hakan laifin INEC ne da ‘yan siyasar yankin.
Sufi ya ce:
"INEC na da hakkin bayyana wa masu ruwa da tsaki dalilin da ya sa ba ta kammala tsarin zaben kamar yadda doka ta tanada ba."
Jama’an Tsanyawa/Kunci sun koka da tsaikon zabe
Wani mazaunin yankin, Muhammad Tsamiya, ya bayyana damuwarsa kan rashin wakilci, inda ya bukaci gwamnan jihar Kano da kada a ci gaba da watsi da mazabar.
Ya na ganin rashin wakilinsu a majalisar zai jawo matsaloli da dama da ta’azzara, rashin abubuwan more rayuwa da su ke fuskanta.
Ya ce:
"Kunchi yanki ne na karkara sosai, har ma malamai da ake tura mana kananan makarantu ba sa zuwa saboda babu hanyoyin mota da kuma ruwan sha, da sauran matsaloli. A siyasa ma, gwamna ne wakilinmu.
Martanin INEC kan tsaikon zaben Tsanyawa
Shugabar Sashen Ilimantar da Masu Zabe da Wayar da Kai ta INEC, Hajiya Safiya, ta yi karin bayani a kan tsaikon da aka samu na gudanar da zaben.
Ta ce da zarar hukumar ta shirya, Kwamishinan Zabe na Jihar Kano, Ambasada Abdu Zango, zai kira taron masu ruwa da tsaki domin tattauna matakan da za a dauka.
'Yan APC ba su maraba da Kwankwaso
A wani labarin, mun ruwaito kungiyar jam'iyyar adawa a Kano NAGG ta APC ta bayyana cewa ko babu Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, sun kammala shirin kwace mulkin Kano daga hannun NNPP.
Kwamared Auwal Shuaib, wanda ya bayyana haka, ya jaddada cewa su na sane da yadda jam'iyyun adawa su ka shiga rudani, saboda haka, kwace mulki zo wa APC cikin sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng