Tankoki 2 Makare da Fetur Sun Fashe a Wani Gidan Mai a Adamawa, Gobara Ta Tashi

Tankoki 2 Makare da Fetur Sun Fashe a Wani Gidan Mai a Adamawa, Gobara Ta Tashi

  • Gobara ta tashi a tashar MRS kusa da filin jirgin sama na Yola, yayin da wasu tankoki biyu dauke da man fetur suka kone kurmus
  • An rahoto cewa jami'an hukumomin kashe gobara na jiha, tarayya da jami'ar AUN sun yi kokarin kashe wutar tare da kare yankin
  • Fashewar tankokin ta faru ne a lokacin da farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya, inda ake fama da matsalar tattali

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Adamawa - Wasu tankoki biyu dauke da man fetur sun fashe a gidan man MRS da ke kan titin Numan kusa da filin jirgin sama a garin Yola.

Rahotanni sun ce an rufe hanyar shiga Yola yayin da mazauna yankin suka fito domin ganin mummunar gobarar, duk da haɗarin da ke cikin hakan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gari gari, sun kashe bayin Allah duk da gwamna ya yi sulhu da su

Rahoto ya yi bayanin yadda tankokin man fetur suka fashe a jihar Adamawa
Tankokin man fetur biyu sun fashe a wani gidan mai a jihar Adamawa. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Tankokin fetur sun fashe a gidan mai a Adamawa

Tankoki biyun sun kone kurmus a lokacin hadawannan rahoto, amma jami'an kashe gobara sun isa wurin domin dakile wutar, inji Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an kashe gobara daga hukumomin kashe gobara na Adamawa, gwamnatin tarayya, da jami'ar AUN ne ke ƙoƙarin kashe wutar.

Haka zalika, an rahoto cewa jami'an tsaro sun isa wurin domin tabbatar da tsaro da hana mutane kusantar inda wutar ke ci.

Yawaitar fashewar tankokin fetur a Najeriya

Gobarar ta faru ne a lokacin da man fetur ya zama abu mai wahalar saye a Najeriya, ƙasar da ke cikin mawuyacin yanayin tattalin arziki.

Kuma wannan na cikin jerin fashewar tankokin fetur da suka faru a jihohi daban daban a farkon shekarar 2025.

A watan Janairu 2025 kawai, an samu manyan haɗurran tankokin mai da suka haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

Tankar fetur ta fashe a gidan mai a Jigawa

Kara karanta wannan

"Zargin baki biyu": Fusatattun mutane sun bankawa gidan basarake wuta a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gobara ta tashi a gidan man Shakkato da ke titin Kiyawa, Dutse, jihar Jigawa, inda ta jawo asarar dukiya mai yawa.

An rahoto cewa gobarar ta tashi ne yayin da wata tankar fetur ta fashe tare da kamawa da wuta a cikin gidan man da yammacin Alhamis, 30 ga Janairu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel