Masu Koyo da Haddar Kur'ani Mai Girma Za Su Samu Gata, Gwamnatin Kano Ta Faɗi Shirinta
- Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagoranci Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bayyana shirinta na ƙara inganta karatun Al-Kur'ani mai girma
- Kwamishinan ilimi, Dr. Ali Makoɗa ya ce gyara tsarin ilimin littafi mai tsarki na ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnati mai ci ta sa a gaba
- Gwammatin Kano ta ɗauki nauyin taron yaye ɗaliban da suka haddace Al-Qur'ani a makarantar sakandiren gwamnati ta hadda a Kiru
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na inganta tsarin neman ilimin Al-Qur’ani mai girma a faɗin ƙananan hukumomi 44.
Gwamnatin karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bayyana shirinta na samar da kyakkyawan yanayi da zai bai wa dalibai damar koyon Al-Kur'ani cikin kwanciyar hankali.

Source: Facebook
Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Dr. Ali Makoda, ne ya bayyana hakan ranar Talata, 4 ga watan Fabarairu, 2025, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta ba iimin Al-Kur'ani muhimmanci
Ya ce ilimin Qur’ani yana daga cikin manyan abubuwan da wannan gwamnati ke bai wa muhimmanci, domin kara karfafa haddar Qur’ani da koyar da addini ga matasa.
A wata hanya ta tallafawa daliban da suka sadaukar da kansu wajen haddace Al-Kur’ani, gwamnatin ta dauki nauyin bikin yaye daliban da suka haddace Qur’ani daga makarantar sakandaren gwamnati da ke Kiru.
Wannan mataki yana daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin Kano ke aiwatarwa don karfafa ilimin addinin Musulunci a jihar Kano.
Al-Kur'ani zai gyara ɗabi'un matasa
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ya ce ce karatun Al-Kur’ani na da muhimmanci wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’ummar Musulmi.
Ya kara da cewa inganta hanyoyin neman ilimin Littafi Mai Tsarki zai taimaka wajen gina tarbiyya da kyawawan dabi’u a tsakanin matasa.
Bugu da kari, gwamnatin jihar Kano ta hade tsarin Islamiyya, haddar Qur’ani da Tsangaya domin tabbatar da cewa yara da matasa sun samu ingantaccen ilimin addini tare da na zamani.
Wannan matakin zai taimaka wajen samar da ilimin da zai ba matasa damar zama masu dogaro da kai, tare da kaucewa aikata laifufuka da rashin aikin yi.
A karshe, gwamnatin Kano ta sha alwashin ci gaba da daukar matakai da za su kara bunkasa neman ilimin da tsarin haddar Al-Qur’ani a jihar.
Su wanene za su ɗauki nauyin taron Al-Kur'ani?
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Izala na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana waɗanda za su iya ɗaukar nauyin taron Al-Qur'ani da za a yi.
Bala Lau ya ce Izala ta na da masallatan Juma'a sama da 15,000 a faɗin Najeriya, idan ta nemi kowane masallaci ya ba da N10,000 ba ƙaramin kuɗi za a tara ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

