Rahoto: Yadda Aka Kashe Jami'an 'Yan Sanda, NSCDC, NIS da Sojoji 326 a Najeriya
- Jami’an tsaro 326 sun mutu tsakanin Janairu 2023 da Janairu 2024, ciki har da ƴan sanda, sojoji, NSCDC da hukumar shige da fice
- Rundunar ƴan sanda ta fi asarar jami’ai, inda aka kashe jami’ai 258, yayin da hukumar NSCDC ta rasa jami’ai biyar a 'yan tsakanin
- Rahoton da aka fitar ya nuna cewa an kashe sojoji 22 a Janairun 2025, yayin da wasu 17 suka mutu a wani hari a Delta a 2024
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Akalla jami’an tsaro 326 ne aka ce sun rasa rayukansu yayin gudanar da aikin su a tsakanin Janairun 2023 zuwa Janairun 2024.
Jami’an da aka kashe sun fito daga hukumomin tsaro daban-daban, ciki har da ƴan sanda, NSCDC, hukumar shige da fice, da sojojin Najeriya.

Source: Facebook
'An kashe sama da jami'an tsaro 326' - Rahoto
Sai dai rahoton da jaridar Punch ta fitar ya ce akwai yiwuwar adadin na iya wuce 326, tun da an tattara alkaluman ne daga rahotannin kafafen watsa labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa rundunar ƴan sanda ce ta rasa jami’ai mafi yawa, inda aka kashe 'yan sanda 258 a tsakanin 2023 zuwa 2024.
A bangaren rundunar sojoji, da ta hada da ta rundunar sojin kasa, sama da ruwa, an rasa sojoji 59, yayin da NSCDC ta rasa jami’ai biyar.
Yadda aka kashe sojoji da dama a Najeriya
Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ita ce ta samu ƙarancin hasarar jami'ai, inda aka kashe jami’anta hudu, a cewar rahoton.
Da rahoton ya fadada bayani, an ji cewa a watan Janairun 2025, an kashe sojoji 22 a wata mummunar arangama da ƴan ta’adda.
A watan Maris din 2024 kuwa, an kashe sojoji 17 a harin ƴan bindiga a garin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.
'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 21
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 21 a wani mummunan harin kwantan ɓauna da ya faru a jihar Katsina.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki
An kashe dakarun haɗin guiwa 21, waɗanda suka haɗa da sojojin Katsina da ‘yan banga, a lokacin harin da aka kai a kauyen Baure, ƙaramar hukumar Safana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
