"Zargin Baki Biyu": Fusatattun Mutane Sun Bankawa Gidan Basarake Wuta a Jihar Kano
- Fusatattun mutane sun ƙone gidan Mai Gari a kauyen Rimin Zakara da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Ƙano
- Rigima ta kaure a garin ne sakamakom rushe gine-ginen jama'a da hukumomin gwamnati suka yi, wanda ya fusata mazauna yankin
- Har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan ƙone gidan basaraken amma ana tsammanin tuni hukumomin tsaro suka fara ɗaukar matakai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - A daren Lahadi, wasu fusatattun mutane sun cinna wa gidan Mai Garin kauyen Rimin Zakara wuta bayan rikici ya ɓarke tsakanin jami’an tsaro da mazauna yankin.
Wannan tashin hankali ya biyo bayan yunkurin rushe gine-gine da ake zargin an yi su ba bisa ƙa’ida ba a yankin, wanda hakan ya haddasa ce-ce-ku-ce tsakanin jama’a da mahukunta.

Asali: Original
Abin da ya haddasa rigima a Kano

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun shiga gari gari, sun kashe bayin Allah duk da gwamna ya yi sulhu da su
Rahoton Aminiya ya nuna cewa rigimar ta samo asali ne daga matakin da jami’an Hukumar Tsara Birane ta Kano (KNUPDA) suka ɗauka na rushe gine-ginen da ke kusa da filin Jami’ar Bayero.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin, waɗanda suka fusata da wannan mataki, sun fito domin nuna adawa da rushe gidajensu.
Majiyoyi da dama daga yankin sun nuna cewa galibin gidajen da aka rusa hukumar KNUPDA ta shafa masu fenti, alamar da ke nuna aiki zai biyo ta kansu.
Sai dai hakan ya jawo arangama da jami’an tsaro, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane huɗu.
Mutane sun ƙona gidan basarake
Bayan aukuwar wannan tashin hankali, wasu da ba a san ko su waye ba sun fantsama gidan Mai Garin suka cinna masa wuta, wanda ya ƙone kurmus.
An ruwaito cewa Mai Garin da sauran iyalansa sun tsere domin tsira da rayuwarsu.
Wasu shaidu sun bayyana cewa ana ganin kona gidan mai garin a matsayin martani kan yadda aka rushe gine-ginen ba tare da sassauci ba.
Hukumomi dai har yanzu ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, amma ana sa ran za a gudanar da bincike don gano hakikanin dalilin kona gidan mai garin da kuma matakan da za a ɗauka kan hakan.
Kotu ta yankewa mutum 5 hukuncin kisa
A wani labarin, kun ji cewa kotun Kano ta yanke mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama su da laifin kashe wata mata da suka kira mayya.
Wadanda ake tuhuma sun rutsa matar a gonarta da ke garin Dadin Kowa a ƙaramar hukumar Wudil, suka daba mata wuka har ta mutu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng