Muhimman Abubuwa 6 da Tinubu Ya Yi wa 'Yan Najeriya a Watan Farko na 2025

Muhimman Abubuwa 6 da Tinubu Ya Yi wa 'Yan Najeriya a Watan Farko na 2025

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta cimma wasu nasarori da suka shafi 'yan Najeriya a watan farko na shekarar 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A bisa dukkan alamu gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta shiga shekarar 2025 da kafar dama.

A watan Janairun 2025 da ya wuce gwamnatin tarayya ta cimma wasu muhimman abubuwa da suka hada da rattaba hannu kan dokar samar da jami'a a jihar Kaduna.

Bola Tinubu
Ayyukan da Tinubu ya yi a watan farkon 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin abubuwa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar a watan Janairun da ya wuce kamar yadda ta wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwa 6 da Tinubu ya yi a 2025

1. Kafa jami'a a Kaduna

Legit ta rahoto cewa Kashim Shettima ya sanar da kafa jami'a a Kudancin Kaduna yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Rabaran Kukah bisa rasuwar Mai martaba Yohanna Sidi Kukah.

Kara karanta wannan

Oluremi Tinubu ta ji kan mutanen Neja, ta ba da tallafin N100m

Wata sanarwa ta tabbatar da cewa Shettima ya yi bayanin ne bayan Bola Tinubu ya amince da kafa jami'ar.

Kashim Shettima ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen ganin an kawo ci gaba a Kudancin Kaduna, musamman a fannin tsaro.

Shettima
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima. Hoto: Aso Villa
Asali: Facebook

2. Yarjejeniyar sadarwa da WIOCC

Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanin West Indian Ocean Cable Company (WIOCC) domin haɗa gidaje miliyan 3 a Najeriya da fasahar intanet.

Ministan Sadarwa, Dr Bosun Tijani, ne ya sa hannu a madadin gwamnati yayin wani taro da aka gudanar a birnin Abuja.

Daily Trust ta wallafa cewa Shugaban Harkokin Kasuwanci na WIOCC, Mista Darren Bedford ne ya sa hannu a madadin kamfaninsu.

Yarjejeniya za ta tabbatar da haɗa wayoyin sadarwa a gidaje, makarantu, asibitoci da ofisoshin gwamnati a Najeriya domin samar da ingantaccen sabis na intanet.

Bosun Tijani
Ministan sadarwan Najeriya, Bosun Tijani. Hoto: Federal Ministry of Information and Digital Economy
Asali: Twitter

3. Kaddamar da shirin lafiya ga matasa

Kara karanta wannan

Naja'atu: El Rufa'i ya tono bayanai kan zargin rashawa da Ribadu ya yi wa Tinubu a 2006

A kokarinta na kawo sauyi ta hanyar kirkire-kirkire a bangaren lafiya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin shekara daya ga matasa a fannin kiwon lafiya.

Za a gudanar da wannan shiri ne ta ofishin da ke da alhakin tsara hadin gwiwar zuba jari a bangaren sabunta lafiyar Najeriya a karkashin Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya.

Gwamnatin tarayya ta ce shirin zai ba matasa damar shiga harkar lafiya a dukkan kananan hukumomin Najeriya.

4. Canza fasalin N-Power

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin sake fasalin shirin N-Power gaba ɗaya domin ƙara inganta tasirin shirin ga al’umma.

Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dr. Nentawe Yilwatda, ne ya bayyana hakan, inda ya zayyana muhimman matakan da aka ɗauka domin sauya tsarin shirin.

Bugu da ƙari, Shugaba Tinubu ya amince da fitar da kuɗi har ₦32.7bn domin aiwatar da shirin jnin kai na NSIP a shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya

Tinubu
Gwamnatin tarayya ta sauya fasalin N-Powe. Hoto: Bayo Onanuga| N Power
Asali: UGC

5. Kaddamar da rajistar matasa manoma

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shafi don rajistar matasa manoma, wani mataki da aka ɗauka domin magance ƙaruwar rashin aikin yi da rashin isasshen abinci a ƙasar nan.

Ministan Matasa, Ayodele Olawande ne ya sanar da ƙaddamar da shafin a wani biki da aka gudanar a Abuja.

Ministan ya bayyana cewa shirin na da nufin samar da ayyukan yi kai tsaye har miliyan 6 ga matasa a shekarar 2025 a fannoni kamar noma, sarrafa abinci, da masana’antu.

Ya ƙara da cewa shafin zai ba matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 damar samun horo kan sabbin dabarun noma, tallafin kuɗi da sauran albarkatu domin bunƙasa harkar noma.

Ministan matasa
Ministan matasan Najeriya a wani taro. Hoto: Ayodele Olawande
Asali: Twitter

6. Biyan hakkokin tsofaffin ma'aikata

Gwamnatin Tarayya ta saki kuɗi har Naira biliyan 22 domin biyan fansho na tsofaffin ma’aikatanta da suka yi ritaya tsakanin Oktoba 2023 da Janairu 2024.

Kara karanta wannan

"A ajiye duk manufar da za ta wahalar da talaka," Gwamna ya soki tsare tsaren Tinubu

Business Day ta wallafa cewa biyan ya mayar da adadin kuɗin da aka fitar zuwa yanzu daga kasafin kuɗin 2024 domin biyan haƙƙin 'yan fansho zuwa Naira biliyan 66.

Hukumar PenCom, wacce ke sa ido kan harkokin fansho a ƙasar nan, ta bayyana cewa Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OAGF) ne ya saki kuɗin.

Kiran dattawan Katsina ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Katsina ta yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu ta saki tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf.

Kungiyar ta ce matakin kama Farfesa Yusuf da hukumar EFCC ta yi na da alaka da siyasa kasancewar yana cikin masu caccakar gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng