Bayan Ganawa da Gwamnatin Tinubu, NLC Ta Canza Shawara kan Karin Kuɗin Kira a Najeriya

Bayan Ganawa da Gwamnatin Tinubu, NLC Ta Canza Shawara kan Karin Kuɗin Kira a Najeriya

  • Kungiyar kwadago watau NLC ta janye zanga-zangar da ta shirya yi don nuna adawa da karin kudin kira, data da saƙo a Najeriya
  • NLC ta shirya fita zanga-zanga gobe Talata, 4 ga watan Fabrairu, 2025 amma yanzu ta dakatar bayan ganawa da wakilan gwamnatin Tarayya
  • Gwamnati ta amince da kafa kwamitin hadin gwiwa da zai kunshi wakilai biyar daga kowanne bangare domin duba tsarin karin kudin sadarwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a fadin kasar nan domin nuna adawa da karin kudin kiran waya.

Kungiyar NLC ta sanar da shirinta na gudanar da zanga-zangar ne a makon da ya gabata, tana mai bayyana cewa karin kudin zai kara wa 'yan Najeriya wahala.

NLC ta dakatar da zanga zanga.
Yan kwadagon Najeriya sun dakatar da shirin fita zanga-zanga kan karin kudin kira Hoto: NLC
Source: Twitter

NLC ta dakatar da fita zanga-zanga

Kara karanta wannan

Bayan shawarar gwamnoni, majalisa za ta zauna domin tabbatar da kudirin haraji da gaggawa

Sai dai bayan wata ganawa a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a daren Litinin, NLC ta yanke shawarar dakatar da zanga-zangar, Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi ranar Taata, 4 ga watan Janairu, 2025 har sai an kammala tattaunawar da aka fara da wakilan gwamnati.

Da yake magana da manema labarai bayan taron, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce gwamnati ta amince da kafa kwamitin hadin gwiwa domin duba tsarin karin kudin.

Gwammatin Tinubu ta kafa kwamiti

A cewarsa, kwamitin zai kunshi wakilai biyar daga kowanne bangare, kuma ana sa ran zai gabatar da sakamakonsa cikin makonni biyu.

Daily Trust ta rahoto shugaban NLC na cewa:

“Mun jaddada cewa NLC ita ce kungiya mafi girma a Afirka, kuma babu wata tattaunawa da za a yi ba tare da mu ba sannan ta yi tasiri.
“A bisa wannan dalili, sun amince da kafa kwamitin da zai duba dukkan tsarin karin kudin kiran waya domin ɗaukar matakin da zai yi wa kowa adalci.
“Kwamitin zai kunshi wakilai biyar daga kowanne bangare kuma ana sa ran zai gabatar da rahoton aikinsa cikin makonni biyu.

Kara karanta wannan

'Za mu iya': Tinubu ya dauki mataki da Amurka ta janye tallafin yaki da cutar HIV

NLC za ta saurari sakamakon binciken kwamiti

Shugaban NLC, Ajaero ya ƙara da cewa rahoton wannan kwamiti ne zai yanke matakin da za su ɗauka ma gaba.

“Rahoton wannan kwamitin ne zai tantance matakin da za mu dauka na gaba da kuma yadda za mu ci gaba da tattaunawa da gwamnati. Har zuwa lokacin, za mu dakatar da shirinmu."

Ya kara da cewa matakin da kungiyar za ta dauka nan gaba, ko na zanga-zanga, yajin aiki ko kauracewa ayyuka, zai dogara ne da sakamakon binciken kwamitin.

Gwamnatin Tinubu ta kira NLC taro

Tun farko, kun ji cewa gwamnatin Najeriya karkashin Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin hana zanga-zangar da ƙungiyar kwadago ke shirin yi kan ƙarin kuɗin kira.

Wannan ya sa gwamnatin ta gayyaci shugabannin NLC zuwa wurin taron da ta shirya domin tattaunawa kan batun da kuma lalubo hanyar masalaha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262