'Ya Ci Kudin Alhazai': EFCC Ta Cafke Dan Kasuwa a Gombe kan Zargin Damfarar N144m

'Ya Ci Kudin Alhazai': EFCC Ta Cafke Dan Kasuwa a Gombe kan Zargin Damfarar N144m

  • EFCC ta gurfanar da Mustapha Mohammed kan zargin damfarar mutane kudin da suka kai Naira miliyan 144 da sunan kai su Umrah
  • Lauyan EFCC ya nuna cewa Mustapha yana da wasu shari’o’i takwas a kansa da suka shafi zargin damfarar sama da Naira miliyan 20
  • Kotun ta ki bayar da belin Mustapha, inda ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Gombe har zuwa a yanke hukunci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Hukumar EFCC, shiyyar Gombe ta gurfanar da shugaban kamfanin MB Lugga Global Travels and Tours, Mustapha Mohammed, a gaban kotu kan zargin damfarar mutane.

EFCC ta tuhumi Mustapha Mohammed da karɓar Naira miliyan 144.1 daga mutane daban-daban, da sunan zai saya masu tikitin jirgi, biza da masauki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kashe Naira biliyan 885 don ayyukan tituna 10

EFCC ta fadi yadda ta kaya a kotu tsakaninta da wani dan damfara a jihar Gombe
EFCC ta gurfanar da wani Mustaph a kotu kan zargin damfarar N144m. Hoto: @officialEFCC.
Asali: Twitter

EFCC ta gurfanar da dan kasuwa a Gombe

A rahoton da EFCC ta fitar a shafinta na X, hukumtar ta ce ya karɓi Naira miliyan 97 daga Hamza Ibrahim Maina don kai shi Umrah a 2024, amma ya yaudare shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan, an tuhume shi da karɓar Naira miliyan 29 daga Ibrahim Arabia da sunan shirya masa tafiyar Umrah, alhali yana da niyyar ya damfare shi.

Hukumar EFCC ta ce Mustapha Mohammed ya aikata laifuffukan da suka saba wa sashe na 1(1)(a) da 1(2)(a) na dokar yaki da damfara ta 2006.

An nemi a ba da belin Mustapha

Lauyan EFCC, SH Saad, ya bukaci kotu ta saka ranar shari’a tare da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari da ke garin Gombe.

Lauyan wanda ake tuhuma, MZ Gambo, ya roki kotu da ta bayar da belinsa, amma lauyan EFCC ya nuna adawa da wannan bukata.

Kara karanta wannan

Badaƙalar N90m: Laifuffuka 5 da EFCC ke tuhumar tsohon shugaban NHIS ya aikata

SH Saad ya ce akwai wasu korafe-korafe takwas da ake yi wa Mustapha Mohammed kan zargin damfara na kudin da ya kai Naira miliyan 120.8.

Kotu ta umarci a tsare Mustapha a gidan yari

Hukumar EFCC ta ce idan aka ba da belin Mustapha, zai iya tserewa daga Najeriya, wanda zai hana a sake gurfanar da shi.

Mai shari’a TG Ringim ya saurari lauyoyin kowanne bangare sannan ya dage sauraron batun bayar da belin.

Sannan kotun ta umarci a tsare Mustapha Mohammed a gidan gyaran hali na Gombe har zuwa lokacin yanke hukunci.

Laifuffuka 5 da ake zargin Farfesa Usman ya aikata

A wani rahoton, mun ruwaito cewa, EFCC na tuhumar tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf da aikata laifuffuka biyar, wadanda ya musanta.

A wani rahoto da EFCC ta fitar, ta nuna cewa ana zargin Farfesa Usman da ya sayen motar N49m alhalin N30m aka ware mata, sannan ya ba da kwangololi ga dan uwansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.