"Gwamnatin Tinubu Ta Nuna Halinta a kan Babban Zabe Mai Zuwa," Atiku

"Gwamnatin Tinubu Ta Nuna Halinta a kan Babban Zabe Mai Zuwa," Atiku

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa manufofinsa na siyasa
  • Paul Ibe, hadimin Atiku, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na shirin gudanar da zabukan da ke tafe da karfa-karfa
  • Atiku ya kuma caccaki gwamnatin Tinubu kan yadda take mayar da martani game da manufofin kasuwancin Shugaban Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu, yana zarginsa da rashin tsari mai kyau wajen karfafa dimokuradiyya a Najeriya.

A wata sanarwa da hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fitar, Atiku ya zargi Tinubu da rashin shiri ko wata manufa ta inganta tsarin dimokuradiyya a kasar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da kafa sabuwar jami'ar fasaha a Najeriya

Tinubu
Atiku ya zargi Tinubu da shirin karfa-karfa Hoto: Atiku Abubakar/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Arise TV ta wallafa cewa an fadi wannan ne a matsayin martani ga hadimin Shugaba Tinubu, Mista Sunday Dare, inda ya soki wasu shugabannin siyasa saboda sukar gwamnatin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Atiku ya caccaki Tinubu

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa Paul Ibe ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu tana nuna irin hanyar da za ta bi wajen gudanar da zabe mai zuwa.

Ya ce:

"Wannan matsayi na Dare wata matashiya da ke kokarin bata suna da kimar shugabannin siyasa da ke neman ci gaba da gyara Najeriya. A cikin hakan, Dare ya bayyana abin da za a gani a yadda gwamnatin Tinubu ke shirin gudanar da zabukan gaba – a matsayin fafatawa da rikici – ko kuma ci gaba da mummunar siyasar kwace da suka shahara da ita."

Atiku ya soki martanin gwamnatin Tinubu ga Trump

A wani martani daban, Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da rashin sanin ya kamata wajen mayar da martani kan manufofin Shugaban Amurka na baya, Donald Trump, musamman dangane da harkokin kasuwanci na kasa da kasa.

Kara karanta wannan

'Mu hadu a 2027': Tinubu ga yan adawa kan kwace mulkinsa, ya fadi abin da ke gabansa

Sanarwar da Paul Ibe ya fitar ta ce:

"Wannan martani daga bakin Dare yana nuni da yadda gwamnatin Tinubu ke kokarin fassara manufar ‘America First’ ta Shugaba Trump a matsayin kokarin kakaba wa kasashe haraji, kuma wannan zai iya shafar dangantakar Najeriya da Amurka da kuma wasu kasashe da kungiyoyi masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci."

Ya ci gaba da cewa:

"Mun yi Allah-wadai da irin wannan sakaci wajen yin furuci daga bakin kakakin Shugaban Kasa kan wata matsala da ka iya shafar dangantakar Najeriya da kasashen waje. Muna kira ga gwamnatin Tinubu da ta yi abin da take wa’azi da baki, ta rungumi manufofin ‘Nigeria First’ maimakon dogaro da tunanin kai da sauran son zuciya da ke haifar da matsala."

Atiku ya dira a kan gwamntin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Tinubu kan kama fitattun 'yan adawa, Omoyele Sowore da Farfesa Usman Yusuf.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu kaca kaca kan kama Farfesa Yusuf da Sowore

Atiku ya bayyana cewa kama waɗannan mutane ba tare da hujja mai karfi ba, alama ce ta yadda ake ƙoƙarin haramta 'yancin fadar albarkacin baki da kuma hana 'yan adawa damar bayyana ra'ayoyinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel