"Su na Cewa Maulidi Bidi'a ne," Sarkin Kano Ya Yi Raddi a kan 'Qur'an Convention'
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce matukar za a yi 'Qur'an convention' tsakani da Allah SWT da Manzonsa, taron ba zai koma bidi'a ba.
- Ya kara da cewa wadanda ke kiran maulidi bidi’a su ne su ka bijiro da taron mahaddata, don haka bai dace su yanke wa wasu hukunci ba
- Amma a ganin Sarki Muhammadu Sanusi, idan taron zai zama hanyar samun kudin ‘yan siyasa, to lamarin zai koma tsantsar mugun aiki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya tofa albarkacin bakinsa a kan babban taron mahaddata Al-Kur'ani da kungiyar Izala ta bijiro da shi a kasar nan.
Rahotanni sun bayyana cewa za a gayyaci mahaddata daga sassa daban-daban na Najeriya domin su hallara a Abuja, kuma a nan ne za a gudanar da taron addu'a ga kasa.

Source: Facebook
A wani bidiyo da Abubakar Muhammad Inuwa ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sarki Sanusi II ya bayyana cewa ba za su yi wa wanda su ka kirkiro taron hukunci da yadda su ke yi wa sauran Musulmi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa akwai abin da za a duba, kafin a tabbatar da babban taro ya zama bidi'a, ko kuma ya na nan a turbar addinin Musulunci.
Sarki Sanusi II ya yi bayanin 'Qur'an convention'
Sarki Muhammadu Sanusi ya bayyana cewa ba za a kira babban taron mahaddata a Abuja da bidi'a ba, kamar yadda Izala ke kiran maulidi bidi'a.
A kalaman Sarkin:
"Wadanda su ka shirya masu kira ga sunna ne, su ke cewa maulidi bidi'a ne. Ko ba haka ba?
"Amma kuma, Manzon Allah ya yi? Sahabbai sun yi? Tabi'a sun yi? Ka ga a lugga bidi'a ne, in aka yi masu hukunci da abin da su ke fada, to sun zama 'yan bidi'a."
'Ba za mu ce bidi'a ba ne," Sarki Sanusi II
Sarki Muhammadu Sanusi ya bayyana cewa ba za a kira babban taron mahaddata Al-Kur'ani da bidi'a ba, matukar za a gudanar da shi ne saboda Allah da Manzonsa.
Ya bayyana cewa, matuka malaman za su yi amfani da addini ne wajen samun kudi a wajen 'yan siyasa, lamarin ya koma tsantsar bidi'a.
Sarki Sansui ya ce:
"Mu ba za mu ce, taro da aka yi na karatun Al-Kur'ani, in dai don Allah aka yi, mu ba za mu ce bidi'a ba ne. Don karatun Kur'ani ne, duk abin da aka yi na girmama Kur'ani, ko nuna daukakar Kur'ani ko na yada Kur'ani ko fadar martabar Kur'ani, ba za mu ce bidi'a ba ne, mu haramta ba.
Ya kara da cewa amma idan 'yan siyasa ne za su fitar da kudin da za a gudanar da taron, wannan kuma tsakanin mashirya taron da Allah SWT.
NSCIA ta goyi bayan 'Qur'an convention'

Kara karanta wannan
'Mu hadu a 2027': Tinubu ga yan adawa kan kwace mulkinsa, ya fadi abin da ke gabansa
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bayyana goyon bayanta ga taron 'Qur'anic Convention'.
Sakataren majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya ce an shirya taron ne don haɗa kan Musulmin Najeriya da nuna baiwar ilimin Alkur’ani, kuma za a gayyato Musulmi da sassan Najeriya dabam-dabam.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

