Hajjin 2025: Gwamna Radda Ya Gano Hanyar Saukakawa Maniyyata Kashe Kudi
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya buƙaci a kawo tsare-tsaren da za su kyautata jindaɗin Alhazan Najeriya
- Dikko Radda ya buƙaci a rage yawan kwanakin da Alhazan Najeriya ke yi a Saudiyya domin rage tsadar kuɗin Hajji
- Gwamnan ya kuma bayyana cewa a shekarar da ta gabata, faɗuwar darajar Naira ta sanya kuɗin zuwa aikin Hajji sun yi tsada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025.
Gwamna Radda ya buƙaci aiwatar da ingantattun shirye-shiryen gyara da kuma kyautata jin daɗin alhazai a faɗin Najeriya.

Asali: Facebook
Gwamna Radda ya yi wannan kira ne yayin wata ziyarar ban girma da shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya kai masa a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya tuna da iyalan babban jami'in sojan da 'yan Boko Haram suka kashe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Radda ya yi magana kan aikin Hajji
Gwamnan ya jaddada cewa akwai ƙalubale da dama da ke hana aikin Hajji tafiya yadda ya kamata, inda ya buƙaci a samu sauye-sauye masu amfani don inganta ayyukan Hajji.
Da yake nazari kan aikin Hajjin 2024 a Katsina, gwamnan ya bayyana yadda faɗuwar darajar Naira ta ƙara tsadar kuɗin aikin Hajji, yana mai buƙatar a nemo mafita mai ɗorewa.
"A bara, aikin Hajji ya fuskanci manyan matsaloli da suka jefa maniyyata da gwamnati cikin damuwa. Duk da waɗannan ƙalubale, mun samu nasarar tura alhazai kusan 2,700 daga Jihar Katsina."
- Dikko Umaru Radda
Wace shawara Gwamna Radda ya ba da?
Gwamnan ya kuma ba da shawarar rage tsawon lokacin aikin Hajji daga kwanaki 40 zuwa makonni uku ko huɗu domin rage kuɗin aikin Hajjin.
"Ina mamakin dalilin da ya sa ake tilastawa alhazanmu su zauna har kwanaki 40 a Saudiyya bayan Hajji, alhali wasu na sauran ƙasashe sukan kammala aikin Hajji a cikin kwanaki 5 zuwa 7."

Kara karanta wannan
Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki
- Gwamna Dikko Umaru Radda
Har ila yau, gwamnan ya bayyana cewa jihar Katsina ta bayar da gagarumar gudunmawa ga alhazan ta a 2024, inda ta kashe sama da N500m domin sayen dabbobin hadaya, tare da kara kuɗin guzuri daga $400 zuwa $4,500.
NAHCON ta sanar da kamfanonin jigilar Alhazai
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da kamfanonin jiragen samannda za su yi jigilar maniyyaya a shekarar 2025.
Hukumar NAHCON ta cimma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama guda huɗu domin kai Alhazan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki.
Asali: Legit.ng