Bidiyo: An Yiwa Dan Najeriya Tiyata, An Ciro Kulli 57 na Hodar Iblis daga Cikinsa

Bidiyo: An Yiwa Dan Najeriya Tiyata, An Ciro Kulli 57 na Hodar Iblis daga Cikinsa

  • Jami’an hukumar NDLEA sun kama Chijioke Igbokwe a filin jirgin Lagos bayan gano yana dauke da hodar Iblis a cikin cikinsa
  • An gaggauta yi wa dan kasuwar tiyata bayan da hodar Iblis guda 57 suka makale masa a ciki kuma ba zai iya fitarwa da kansa ba
  • Gaba ɗaya, an fitar da hodar Iblis guda 81 daga jikinsa, wanda nauyinsu ya kai kilogiram 1.943 kamar yadda NDLEA ta yi karin bayani

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - A wani yanayi mai cike da hatsari, an yiwa wani ɗan kasuwa, Chijioke Nnanna Igbokwe, tiyata, an cire kullin hodar iblis 57 daga cikinsa.

An rahoto cewa an yiwa dan kasuwar mai shekaru 59 tiyatar laparotomy don fitar da hodar bayan kwana bakwai da hadiyarta a Addis Ababa, Habasha.

Kara karanta wannan

Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

NDLEA ta yi magana da ta kama dan kasuwa dauke da kulli 81 na hodar iblis a cikin cikinsa.
NDLEA ta kai dan kasuwa asibiti, an yi masa tiyata tare da ciro kulli 57 na hodar iblis. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

NDLEA ta kama dan kasuwa ya hadiye hodar iblis

A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, NDLEA ta ce ta kama shi a filin jirgin Murtala Muhammed a Legas yayin da yake dawowa daga Habasha a ranar Lahadi, 25 ga Janairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken jiki da aka yiwa dan kasuwar ya bayyana cewa yana ɗauke da miyagun ƙwayoyi a cikin cikinsa, inda aka kwashe shi zuwa ofishin NDLEA.

Bayan gudanar da bincike, an ce Igbokwe, wanda ya ce yana kasuwancin kaya a kasuwar Arena, Oshodi, ya bar Legas zuwa Addis Ababa a ranar 22 ga Janairu.

Dan kasuwar ya hadiyi hodar iblis saboda $3,000

A can Addis Ababa, ya hadiye kullin hodar Iblis guda 81 a ranar 23 ga Janairu, sannan ya hau jirgi zuwa Beirut, Labanon, domin kai wa wani kaya don a biya shi $3,000.

Da ya isa birnin Beirut, sai aka hana shi shiga saboda bai da $2,000 da ake buƙata domin samun izinin shiga ƙasar.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Daga nan aka mayar da shi birnin Addis Ababa, inda ya yi ƙoƙarin fitar da hodar Iblis daga cikinsa amma bai yi nasara ba.

An fitar da kullin hodar iblis 81 daga cikinsa

Daga bisani, ya hau jirgi zuwa Legas a ranar 25 ga Janairu da miyagun ƙwayoyin har yanzu a cikinsa inda jami’an NDLEA suka kama shi a filin jirgin sama a ranar 26 ga Janairu.

Bayan kwana biyar ana jiran shi ya fitar da ƙwayoyin, ya samu ya yi kashin guda 24 kacal bayan ya samu taimakon likita a asibitin LASUTH.

Saboda lokaci yana ƙurewa kuma yana da wasu matsalolin lafiya, aka garzaya da shi asibiti domin a yi masa tiyata don fitar da sauran ƙwayoyin.

A karshe, an fitar da hodar Iblis guda 81 da nauyinsu ya kai kilogiram 1.943 daga cikinsa.

Kalli bidiyon a nan kasa:

NDLEA ta cafke mata da hodar iblis

Kara karanta wannan

Jigawa: Gwamna zai ciyar da mabukata 189, 000 a Ramadan, an ji kudin da zai kashe

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NDLEA ta cafke wata mata dauke da kulli 35 na hodar iblis a cikin kayanta a filin jirgin saman Legas.

NDLEA ta ce matar mai suna Okafor Ebere Edith ta yi safarar kwayoyin ne a cikin wani jirgin saman Cotevoire zuwa Monrovia, Liberia a filin MMIA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.