NDLEA ta kame wata mata da hodar Iblis kunshe cikin kayanta a filin jirgin sama

NDLEA ta kame wata mata da hodar Iblis kunshe cikin kayanta a filin jirgin sama

  • A filin jirgin jihar Legas, an kame wata mata dauke da hodar iblis kunshe cikin wani boyayyen wuri
  • Matar ta boye hodar iblis din ne cikin kaya da ke jikinta domin gujewa binciken hukuma
  • An kuma kame wani mutum da ke dauke da tabar wiwi kunshe cikin daurin busasshen ganyen goro

Jihar Legas - Hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta cafke wata mata da ta boye hodar iblis a cikin kayanta a filin jirgin saman Legas, The Cable ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi.

Babafemi ya ce wacce aka kamen mai suna Okafor Ebere Edith an kama ta ne a ranar Asabar 31 ga watan Yuli, lokacin da fasinjoji ke fita daga jirgin saman Cotevoire zuwa Monrovia, Liberia daga filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA), Ikeja, Legas.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta kama Saraki kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa

Ya ce matar ta saka hodar iblis guda 35 a cikin kayan ta domin ta guje wa binciken jami'an tsaro a filin jirgin sama.

NDLEA ta kame wata mata da hodar Iblis kunshe cikin kayanta a filin jirgin sama
Matar da aka kame da hodar iblis | Hoto: lailasnews.com
Asali: UGC

Babafemi ta ce:

"A lokacin hira ta farko, ta yi ikirarin burinta na son tayi kudi ya kai ta ga fataucin miyagun kwayoyi."

An kame wani fasinja da tabar wiwi kunshe cikin busasshen ganyen goro

Mista Babafemi ya ce jami'an sun kuma kama wani wanda ake zargi, Echendu Jerry Maduakolam, wani fasinjan da ke son zuwa Istanbul, a zauren fita na filin jirgin MMIA a ranar 27 ga watan Yuli, Premium Times ta tattaro.

Ya ce, an kama wanda ake zargin ne a lokacin da kamfanin sufurin jiragen sama na Masar da ke kan hanyarsa ta zuwa Turkiyya ke tantancewa, an kama shi da giram 78 na tabar wiwi hade da busasshen ganyen goro.

NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta

Kara karanta wannan

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

A wani labarin, Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Brazil, Misis Anita Ugochinyere Ogbonna, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA) dake Abuja, dauke da kwalayen hodar iblis 100 da ta boye a al'aurarta da jakarta.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fada a ranar Lahadi a Abuja cewa an kama matar mai 'ya'ya uku ne a daren Juma’a lokacin da suka isa Abuja ta jirgin Qatar Air daga Sao Paulo na Brazil ta Doha babban birnin kasar Qatar.

A cewarsa, yayin binciken kwakwaf, an ciro hodar iblis 12 da ta saka a al'aurarta yayin da aka gano wasu kunshi 88 da aka saka a cikin safa a boye cikin jakarta, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel