Kowa Ya Shirya: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Lokacin Kara Kudin Wutar Lantarki
- Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa nan da 'yan watanni masu zuwa za a sake kara kudin wutar lantarki ga dukkanin 'yan kasar
- Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan makamashi ta ce dole ne a kara kudin domin ba ci gaba da samar da wutar a Najeriya
- A zantawarsu da Legit Hausa, wasu mazauna Kaduna, sun nuna rashin amincewarsu da hakan, suna ganin cewa za a kara kuntata talaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tanzaniya - Olu Verheijen, mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan makamashi, ta ce za a kara farashin wutar lantarki a Najeriya cikin watanni masu zuwa.
Idan ba a manta ba, a ranar 3 ga Afrilun 2024, gwamnatin tarayya ta amince da ninka kudin wuta sau uku ga masu abokan hulda 'yan Band A.

Asali: Twitter
Gwamnati za ta kara kudin wutar lantarki
A cewar rahoton Bloomberg, Verheijen ta yi wannan bayani ne a taron shugabannin kasashen Afrika kan makamashi a Dar es Salaam, Tanzaniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Verheijen ta bayyana cewa ya kamata a kara kudin wuta da kashi 66 domin ya dace da ainihin kudin samar da lantarki ga masu amfani da ita.
Mai ba shugaban kasar shawara ta jaddada cewa dole ne a kara kudin domin inganta samar da wutar da wutar da jawo masu zuba jari.
Dalilin gwamnati na son kara kudin wutar
Verheijen ta ce Najeriya na kokarin tabbatar da tsarin biyan kudin wuta da zai jawo masu zuba jari ba tare da cutar da talakawa ba.
"Daya daga cikin manyan matsalolin da muke kokarin warwarewa ita ce samar da kudin da zai jawo hannun jari cikin masana'antar wuta," inji Verheijen.
Ta kara da cewa hakan zai tabbatar da samun kudaden shiga domin ci gaba da inganta samuwar wutar lantarki a kasar.
Mazauna Kaduna sun yi adawa da hakan
Legit Hausa ta tattauna da wasu mazauna Kaduna, domin jin ra'ayinsu kan wannan kuduri na gwamnati na kara kudin wutar lantarki da kusan kashi 66%.
Hussaini Baban Nur, ya ce ba ana adawa da kara kudin wutar lantarki haka kurum ba, ana yi saboda ko an kara kudin, wutar ba ta zama.
"A gidana, ina biyan N7,000 duk wata, amma ina tabbatar maka sai tsakiyar dare suke kawo wutar, da rana idan sun kawo, ba ta wuce awa daya, wasu ranakun ma haka muke wuni babu wutar."
Hajiya Balaraba da ke sana'ar Kankara a kusa da makabartar layin Mallam Bello, ta ce yanzu ta jingine na'urorin daskarar da ruwa saboda rashin wuta.
"Tun a shekarar da wuce muke fuskantar rashin wuta. 'Yar sana'ar da nake yi ta kankara yanzu na daina saboda ko na kulla kankarar ba ta daskarewa.
"Ruwa ne kawai na san yana yin sanyi saboda sukan maido wuta da tsakar dare. Ranar da ba su maido ba kuma to ranar ba zan iya sayar da ruwan ledar ba."

Kara karanta wannan
Badakalar N110bn: Shaidun EFCC sun kada hantar lauyan tsohon gwamna, Yahaya Bello
Wani Alhaji Sama'ila da muka zanta da shi, ya roki gwamnati da ta rika tilasta kamfanonin rarraba wutar samar da ita, domin kara kudin wuta ba tare da samuwar wutar ba zai kara jefa talaka a mawuyacin hali.
Zanga zanga ta hana gwamnati kara kudin wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ce ana kashe N120 don samar da kilowatt ɗaya na wutar lantarki a kowacce awa.
Ministan wuta, Cif Adebayo Adelabu, ya ce kudin da 'yan Najeriya ke biya bai kai yawan da ake kashewa wajen samar da wuta ba.
Ya bayyana cewa ma’aikatar wuta ta shirya ƙarin farashin wuta, amma zanga-zangar da aka yi ta hana aiwatar da sabon tsari.
Asali: Legit.ng