Matawalle: Sukar Tsohon Gwamna Ta Sanya an Taso Ministan Tinubu a Gaba
- Gargaɗin da Bello Matawalle ya yi wa Rotimi Amaechi, bai yi wa wani jigon APC a jihar Rivers daɗi ba
- Cif Eze Chukwuemeka Eze ya bayyana gargaɗin da ƙaramin ministan tsaron ya yi wa tsohon gwamnan na jihar Rivers, a matsayin abin da bai dace ba
- Ya buƙaci Matawalle da ya mayar da hankali wajen samar da tsaro maimakon yi wa masu sukar gwamnati barazana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Rivers kuma amini ga Rotimi Amaechi, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya yi wa Bello Matawalle martani kan sukar tsohon gwamnan.
Cif Eze Chukwuemeka Eze ya tsaya tsayin daka wajen kare Rotimi Amaechi, wanda ke fuskantar suka daga wasu manyan jami’an gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Twitter
Jaridar Tribune ta ce Eze ya yi Allah wadai da gargaɗin da ƙaramin ministan tsaro, Dakta Bello Muhammed Matawalle, ya yi wa Amaechi.

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya tuna da iyalan babban jami'in sojan da 'yan Boko Haram suka kashe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Eze ya bayyana gargaɗin a matsayin wanda bai dace, yana mai kira ga Matawalle da ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro a ƙasar nan maimakon yin barazanar da babu amfanin yin ta.
Jigon APC ya caccaki Matawalle
Jigon na APC ya soki ƙaramin ministan tsaron kan ƙoƙarin hana sukar gwamnati da gangan.
Eze ya jaddada cewa maimakon yin gargaɗi, kamata ya yi Matawalle ya maida hankali kan shawo kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan, musamman a yankin Arewa maso Yamma, wanda ke fama da hare-haren ƴan bindiga.
Haka kuma, Eze ya tunatar da Matawalle rawar da Amaechi da sauran masu kishin ƙasa suka taka wajen kafa APC, yana mai cewa da ba don hangen nesa da sadaukarwar su ba, da ba za a samar da jam’iyyar ba.
Ya bayyana Matawalle a matsayin ɗan ci ma zaune, wanda ke cin moriyar APC ba tare da fahimtar asalin jam’iyyar ko gwagwarmayar da aka sha kafin ta samu nasara ba.
Wace shawara aka ba Matawalle
Jigon na APC ya kuma soki halin da tsaro ke ciki a ƙasar nan, musamman a ƙarƙashin Matawalle a matsayinsa na ministan tsaro.
Ya nuna yadda ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane ke ci gaba da aikata laifuka a jihar Zamfara, mahaifar Matawalle, a matsayin babbar alamar gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaro.
A ƙarshe, Eze ya yi kira ga gwamnati da ta maida hankali kan shawo kan matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta, musamman rashin tsaro, maimakon kokarin toshe bakin masu sukar halin da ƙasa ke ciki.
Amaechi ya ba ƴan Najeriya shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Chibuike Amaechi, ya tunatar da ƴan Najeriya kan abin da suke buƙata domin kawo sauyi a ƙasar nan.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai miƙa mulki cikin ruwan sanyi ba, ba tare da an kai ruwa rana ba.
Ya buƙaci ƴan Najeriya da su tashe su nuna da gaske cewa suna son kawo canji a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng