'Hukuncin da Ya Kamaci Masu Cin Hanci': Inji Yaron Buhari duk da Zargin Rashawa a Lokacinsu
- Tsohon mai ba da shawara ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci a aiwatar da hukuncin kisa ga masu cin hanci da rashawa a Najeriya
- Obono Obla ya ce wannan mataki mai tsauri zai hana mutane aikata rashawa, wanda ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewa
- Obla ya jaddada bukatar inganta hukumomi, inganta gaskiya da rikon amana, tare da hukunta masu aikata laifuffukan rashawa don gyara al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon hadimin ga Muhammadu Buhari ya yi bukaci gurfanarwa da hukuncin kisa ga masu cin hanci da rashawa.
Okoi Obono Obla, ya ba shawarar daukar matakin ne mai tsauri saboda daidaita lamura a Najeriya da samar da ci gaba.

Asali: Facebook
Cin hanci: Tsohon hadimin Buhari ya kawo mafita
Obla bayyana hakan a Calabar yayin jawabinsa a taron tunawa da Ralph Opara karo na 16, wanda Kungiyar NAS ta shirya, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hadimin ya ce hakan na daya daga cikin hanyoyin dakile cin hanci da rashawa da ya yi katutu a kasar.
"Daya daga cikin hanyoyin da za a iya dauka shi ne kafa dokar hukuncin kisa ga wasu nau’ukan cin hanci da laifuffukan kudi.”
“Wannan mataki mai tsauri na iya zama wata hanya ta dakile masu aikata rashawa, don rage illa da wannan dabi’a ke haifarwa a cikin al’umma.”
- Obono Obla
Yadda cin hanci ke hana ci gaban kasa
Obla ya bayyana yadda wasu ‘yan Najeriya ke kokarin kare muradun kasa, yayin da wasu ke cin hanci da rashawa wanda ke hana ci gaba.
Ya jaddada bukatar inganta hukumomi, karfafa gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da cewa masu laifi sun fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan
Tsohon sanata ya zubar da hawaye da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 11
Haka kuma, ya ce akwai bukatar sake duba dabi’un al’umma da ci gaban tunani don magance tushen matsalar rashawa.
Ya kara da cewa dole ne kungiyoyin masu zaman kansu da na farar hula da gwamnati su hada kai wajen gina al'umma mai gaskiya da rikon amana.
Shawarar shugaban kungiyar NAS a Najeriya
A nasa bangaren, Shugaban NAS, Dr. Joseph Oteri, ya ce taron an shirya shi ne don tunawa da Ralph Opara, daya daga cikin manyan ‘yan jarida a Najeriya.
Ya ce suna fatan ci gaba da yada irin tunanin da Opara ya tsaya tsayin daka akai a rayuwarsa.
Ya kuma ce suna fatan wannan taro zai taimaka wajen samar da mafita ga matsalolin da za su iya tsara makomar Najeriya da ci gabanta.
Hadimin Buhari ya soki masu kushe Muslim/Muslim
Kun ji cewa tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya bukaci wadanda suka soki mulkin Muslim-Muslim na Bola Tinubu su nemi gafara.
Bashir Ahmad ya fadi haka ne bayan shugaban CAN na Arewa ya ce Kiristoci na jin dadin mulkin Tinubu a yanzu.
Yakubu Pam ya ce zaluncin da Kiristoci suka fuskanta a gwamnatocin baya ya ragu, yana yabawa Tinubu kan kokarinsa na hada kowa da kowa a mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng