'Yan Bindiga Sun Shiga Kauye cikin Dare Sun Yi wa Mutane Yankan Rago
- Wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kashe mutum biyar a kauyen Lighitlubang da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato
- Shaidun gani da ido sun ce maharan sun kai farmaki ne da dare lokacin da mutanen kauyen ke barci, inda suka yi yankan rago ga wasu mutane
- Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da aika jami'an tsaro domin dawo da zaman lafiya a yankin da abin ya faru
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - Wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kai hari kauyen Lighitlubang da ke cikin gundumar Bungha, ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato, suka kashe mutum biyar.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga kauyen ne da tsakar dare a ranar Juma’a, 31 ga watan Janairu, 2025, lokacin da mazauna yankin ke cikin barci.

Asali: Original
Jaridar Punch ta rahoto cewa cikin waɗanda aka kashe akwai wani mutum da matarsa da ɗansu, tare da wani mutum da matarsa da aka yanka su gaba ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kai harin Filato da dare
Wani mazaunin kauyen da aka kai harin, Moses Bankat, ya tabbatar da faruwar harin ga manema labarai a ranar Asabar.
Mutumin ya ce:
“Harin ya faru ne a daren jiya misalin ƙarfe 12:00 na dare. Wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne suka shiga kauyen Lighitlubang a gundumar Bungha, suka kashe mutum biyar;
Sun kashe wani mutum da matarsa da ɗansu da kuma wani mutum da matarsa, dukkansu an yanka su.”
Shaidu gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shigo kauyen ne ba tare da an gane su ba, suka kuma yi amfani da makamai masu kaifi wajen kashe mutanen.
New Telegraph ta wallafa cewa wani mazaunin kauyen ya ce:
“Ba mu san lokacin da suka shigo ba, sai da muka ji ihu daga gidajen da ke kusa. Da muka kai ɗauki, mun tarar da gawarwaki a wurin,”
'Yan sanda sun tabbatar da kai harin
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro zuwa yankin da aka kai harin.
“Mun tura jami'an tsaro zuwa kauyen da aka kai harin domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron jama'a.
"Haka zalika, an fara bincike kan lamarin domin gano waɗanda suka aikata wannan ta'asa.”
- DSP Alabo Alfred
DSP Alfred ya ƙara da cewa rundunar na jiran ƙarin bayani daga shugaban 'yan sandan yankin (DPO) da jami’ansa, waɗanda suka shiga daji domin bincike.
“Ina jiran cikakken rahoto daga DPO idan suka dawo daga binciken da suke yi a cikin daji,”
- DSP Alabo Alfred
Mazauna yankin sun shiga fargaba
Rahotanni sun nuna cewa wannan hari ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna kauyen da kewaye.
Da dama daga cikinsu sun bayyana damuwa kan yadda hare-haren ke ƙaruwa a yankin ba tare da wani tsayayyen mataki ba.
A baya-bayan nan, yankin ƙaramar hukumar Mangu ya fuskanci hare-hare masu kama da wannan, wanda hakan ke ƙara dagula zaman lafiyar al’ummomin yankin.
Maganar kan kiran sallah a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Filato ta karyata jita jitar cewa Mai girma gwamna ya haramta kiran sallah.
Legit ya rahoto cewa gwamnan ya ce labarin bai tabbata ba, kawai wasu ne suke shirin hada shi fada da al'ummar Musulmi a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng