Wani Bawan Allah da Ya Musulunta Ya Fara Funkantar Matsala da Matarsa a Abuja
- Wani magidanci mai suna Yahaya ya kai ƙarar matarsa gaban kotu a Abuja, ya nemi a raba aurensu saboda banbancin addini
- Ya shaidawa alƙali ya auri matar ne lokacin yana Kirista, daga bisani kuma ya musulunta, tun daga nan zaman lafiya ya bar gidansa
- Ya roki kotun ta raba auren sannan ta ba shi damar riƙe ɗaya daga cikin ƴaƴa biyu da suka haifa a zaman aurensu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wani magidanci mai suna Yahaya ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa, Adenike, bisa dalilin banbancin addini.
Yahaya ya bayyana cewa yana bin addinin Kiristanci lokacin da suka yi aure, amma daga baya ya Musulunta.

Asali: Twitter
Rahoton Tribune Nigeria ya nuna cewa matarsa ta ki aminta su koma addinin Musulinci tare, lamarin da ya haifar da matsaloli a tsakaninsu.

Kara karanta wannan
Rikakken dan bindiga ya tuba daga barna bayan sakin wadanda ya kama, ya sauya suna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magidanci ya fara fuskantar matsala a gida
A cewarsa, wannan banbanci ya sa zamansu ya fara wargajewa, har suka daina samun fahimta da mu'amala a tsakaninsu, suka koma rayuwa kamar baƙi a gida ɗaya.
Baya ga bukatar rabuwa, Yahaya ya roki kotu da ta ba shi damar rike ɗaya daga cikin ‘ya’yansu biyu, yayin da matarsa za ta riƙe ɗayan.
Abin da Yahaya ya faɗawa Kotu
A gaban kotu, Yahaya ya ce:
“Mai shari’a, ba mu yi biki ba lokacin aurenmu, kuma ban biya sadaki ba. A lokacin da muka yi aure, ni Kirista ne, amma daga baya na karɓi addinin Musulunci.
“Matata ta ki yarda da wannan canji, kuma ta hana mu zauna lafiya. Ta daina kula da ni, ta daina yin ayyukan gida, kazanta ta yi yawa a gidan.
“A yanzu, babu fahimtar juna a tsakaninmu kuma ba mu ma cika magana da juna ba. Muna rayuwa ne kamar baƙi a gida guda.
Buƙatun da magidancin ya nema a kotu
Magidancin ya roki alkalin kotun ya kashe auren, sannan ya raba masu ƴaƴa biyu da suka haifa a zaman aurensu.
“Ina rokon wannan kotu mai daraja da ta raba aurenmu kuma ta bani damar riƙe ɗaya daga cikin ‘ya’yanmu biyu, matata ta riƙe ɗayan.
"Zan kuma rika ba da N10,000 duk wata domin ciyar da yaron da ke tare da ita," in ji shi.
Bayan sauraron karar, alkalin kotun, Mai shari'a S.M. Akintayo, ta daga shari’ar zuwa wani lokaci na gaba.
Magidanci ya yi barazanar faɗawa rijiya
A wani rahoton, kun ji cewa wani magidanci, Mista Isiaka Azeez ya nemi kotu ta raba aurensa da mai ɗakinsa bayan shekaru 40 suna tare.
Azeez ya yi barazanar cewa zai fada rijiya idan kotun ba ta amince da bukatarsa ta neman raba auren ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng