Zan fada rijiya idan ba a raba aurena da ita ba - Miji ya fada a kotu

Zan fada rijiya idan ba a raba aurena da ita ba - Miji ya fada a kotu

Wani tsohon ma'aikacin gwamnati, Mista Isiaka Azeez, ya nemi kotun garajiya da ke zamanta a yankin Mapo na garin Ibadan a jihar Oyo da ta raba aurensa da matarsa, Mujidat, bayan shafe tsawon shekaru 40 suna tare.

Azeez ya yi barazanar cewa zai fada rijiya idan kotun bata amince da bukatarsa ta neman raba auren ba, saboda fusata shi da ya ce Mujidat na yi koda yaushe.

Da yake fada wa alkalin kotun, Mista Ademola Odunade, irin mawuyacin halin da ya tsinci kansa, Azeez ya ce ya gaji da matsalolin matarsa da kuma irin barazanar da take yi wa rayuwarsa.

Azeez, mai shekaru 70, ya ce bai taba samun farin ciki da jin dadi a cikin aurensa na tsawon shekaru 40 da ya yi da Mujidat ba, ya ce bayan bakin ciki da kuncin rayuwa babu abin da zai adar a zamansa da matarsa.

"Fiye da shekaru 20 kenan yanzu mu na rayuwa irinta mage da bera a tsakanina da Mujidat, don bata da ladabi ko kadan, na yi nadamar aurenta.

"Tun da ta fahimci al'amura sun sauya min, babu kudi a hannu na, ta fara kawo min raini tare da kuntata min.

DUBA WANNAN: Shekaru 15 ba haihuwa: Wata mata ta haifi 'yaya 4 a Bauchi, ta roki gwamna ya taimaka ya bata aiki

“Har 'ya'yan mu da muka haifa ta fada musu cewa ni ba komai bane, yanzu sun raina ni, saboda ko gaishe ni basa yi.

"Yanzu an shafe fiye da shekara guda kenan da Mujidat ta tattara kayanta ta bar gida na.

"Idan wannan kotu bata raba aurenmu a yau ba, na gwammaci na je na fada a cikin kogin 'Dandaru'," a cewar Azeez.

Sai dai, Mujidat ta musanta wasu daga cikin zarge-zaregen da Azeezat ya yi mata tare da rokon kotun da kar ta raba aurensu, ko don saboda 'ya'yan da suka haifa.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya raba auren tare da bayyana cewa alaka tsakanin ma'auratan ta yi lalacewar da ba zata gyaru ba.

Odunade ya bukaci Azeez ya biya Mujidat N5,000 a matsayin kudin da zata biya domin kwashe sauran kayanta da ke gidansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel