Ana nema a raba aure a dalilin yawan karatun Mai gida a Kasar Indiya

Ana nema a raba aure a dalilin yawan karatun Mai gida a Kasar Indiya

Yayin da labari ke yawo a gari, wata Baiwar Allah ta nemi hukuma ta raba auren ta saboda Mijinta ba ya sallah, mun samu wanda ta kawo kukan cewa na ta Mai gidan ya cika mugun karatu.

A wani lamari mai ban mamaki, wata Baiwar Allah a Garin Bhopal a kasar Indiya, ta dumfari wani karamin kotu domin a raba aurenta da Mijinta inda ta ce Mai gidan na ta bai da aiki sai karatu.

Wannan Baiwar Allah ta sanar da hukuma cewa shirya jarrabawar UPSC ta sa Mai gidan ta ba ya komai illa karatu. Abin dai ya kai daidai da magana, wannan mutumi ba ya yi wa Maidakinsa.

Kamar yadda indiatoday.com ta rahoto, wannan Mata da su ke zaune a Yankin Katara Hills ta roki Mai gidan ta ya rika fita da ita zuwa wajen shakatawa ko gidan kallon fim, amma ya ki amincewa.

Bugu da kari, wannan Matar aure ta sanar da wata cewa Mai gidan na ta ba ya zuwa gaida ‘yanuwansa. Wannan ya sa aka nemi a zauna da wannan Mai gida domin kokarin shawo kansa.

KU KARANTA: Miji na ba ya sallah don haka a raba auren - Ta fadawa kotu

A lokacin da aka nemi ayi sulhu Mai gidan wannan Baiwar Allah, ya nuna cewa babu abin da ya hada shi fada da ita, illa kurum ya dage ne da karatunsa domin ya samu ya ci jarrabawar UPSC.

Wannan Bawan Allah ya ke cewa tun yana yaro bai da buri irin ya lashe wannan jarrabawa don haka ya ke bukatar isasshen lokaci domin ya yi karatu don ya samu nasara a wannan takarda.

Har ila yau, wannan Mai gida ya sanar da Matar da ke kokarin shawo kansa da Mai dakin sa cewa rayuwar aurensa ta na tangal-tangal don haka ba zai so wani abu ya sake kawo masu cikas ba.

Bayan sauraron wannan ma’aurata, wannan Mata mi kokarin raba gardama ta nemi Mata da Mijin su sake zama domin shawo kan matsalolinsu. An shawarci matar ta hakura da maganar saki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel