Gwamna a Najeriya Ya Samu Nasara, Ya Zama Shugaban Gwamnonin Yankin Tafkin Chadi

Gwamna a Najeriya Ya Samu Nasara, Ya Zama Shugaban Gwamnonin Yankin Tafkin Chadi

  • Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Tafkin Chadi a taron da aka yi a Maiduguri
  • Buni ya yi alkawarin aiki tare da gwamnonin kasashen da ke kewaye da Tafkin Chadi domin magance matsalar ta’addanci, fatara, da matsalolin ‘yan gudun hijira
  • Ya bukaci tallafi daga gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa domin inganta tattalin arziki, noma, kiwo, da ci gaban al’ummar yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya zama sabon shugaban Kungiyar Gwamnonin Yankin Tafkin Chadi.

An zabi Mai Mala Buni ne a taron kungiyar da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Gwamna Mala Buni.
Gwamna Buni ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin tafkin Chadi Hoto: @Dr_ahmadsmall
Asali: Twitter

Bayan zabensa, Gwamna Buni ya gode wa takwarorinsa bisa wannan dama da suka ba shi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ba za ta raga ba," Abba Gida Gida ya zare takobin yaki da rashawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Buli ya jero abubuwan da zai yi

Ya tabbatar da cewa zai yi aiki tukuru don tabbatar da hadin gwiwa da ci gaba a yankin tafkin Chadi wandabke fama da ƙalubalen tsaro.

Gwamna Buni ya ce yana da burin inganta zaman lafiya da tsaro, musamman a wuraren da matsalolin tsaro suka fi kamari.

Kungiyar tana da burin hada kai da gwamnonin jihohi da kasashen da ke kusa da tafkin Chadi domin magance matsalolin tsaro, musamman yaki da kungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da ISWAP.

A yayin jawabinsa, Gwamna Buni ya jaddada cewa zai yi aiki kafada da kafada da gwamnonin kasashen da ke kewaye da Tafkin Chadi domin bunkasa tattalin arziki, zaman lafiya da ci gaban yankin.

Buni ya tallafawa yankin tafkin Chadi

Ya kuma yi kira ga gwamnatoci da hukumomi na kasa da kasa da su ci gaba da taimakawa domin ganin yankin ya samu ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa

Mala Buni ya ce shugabancinsa zai mayar da hankali kan yaki da fatara, inganta noma da kiwo, da kuma tallafawa ‘yan gudun hijira da matsalar tsaro ta shafa.

Ya kuma yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa jajircewarsa ga zaman lafiya, tsaro, da ci gaban yankin tafkin Chad.

A rahoton Leadership, Mala Buni ya ce:

“Muna fatan samun ƙarin haɗin gwiwa mai ƙarfi, goyon baya, da isassun kuɗi domin mu cimma burinmu na gina yankinmu da inganta rayuwar al'ummarmu."

Gwamna Buni ya rabawa talakawa kuɗi

Kun ji cewa Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya kai ziyarar ba zata domin duba aikin titin Damaturu zuwa Kalallawa.

Yayin wannan ziyara, gwamnan ya taimakawa ma'aikata da wasu talakawa masu aikin sarar itace da kuɗi domin karfafa masu guiwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel