Bauchi: Ana Zargin Kwamishina da Sace Yarinya, Wanda Ake Tuhuma Ya Fayyace Lamarin

Bauchi: Ana Zargin Kwamishina da Sace Yarinya, Wanda Ake Tuhuma Ya Fayyace Lamarin

  • Kwamishinan Ruwa a jihar Bauchi, Abdulrazak Nuhu Zaki, ya musanta zargin satar yarinya, yana mai cewa Zainab diyarsa ce ta jini kuma yana da hakki a kanta
  • Zaki ya bayyana cewa ya rabu da mahaifiyarta ne saboda matsin lamba daga danginta, duk da kokarin wasu wajen daidaita rikicin auren
  • Ya ce kotuna uku sun yanke hukunci a kansa, amma ana hana shi ganin diyar, har sai da ta yanke shawarar komawa wajensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Bauchi - Ana zargin Kwamishinan Ruwa na Jihar Bauchi, Abdulrazak Nuhu Zaki da dauke wata yarinya mai suna Zainab.

Sai dai kwamishinan ya bayyana zargin da wata Iklima Manu Soro ta yi a kansa na satar yarinya a matsayin maras tushe.

Mata ta shigar da kwamishina kotu kan zargin satar yarta
Kwamishina a jihar Bauchi ya musanta zargin satar yarinya inda ya ce yar cikinsa ce. Hoto: Abdulrazak Nuhu Zaki.
Asali: Facebook

Kwamishina ya musanta zargin sace yarinya

Kara karanta wannan

"Na tuba, ba zan kara ba": Kasurgumin dan ta'adda na so gwamnati ta yi masa afuwa

Tribune ta ce yayin mayar da martani kan korafin da aka shigar, Zaki ya musanta zargin inda ya ce 'yarsa ce ta cikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ta yaya zan sace diyar jikina? Zainab diyata ce.

- Cewar kwamishinan

Nuhu Zaki ya bayyana cewa sun yi aure da mahaifiyarta a bisa dokar Musulunci, amma dalilin matsin lamba daga danginta ne suka rabu da juna.

“Ba ni da niyyar rabuwa da matata saboda muna son juna, amma ‘yan uwanta sun matsa mata lamba har ta fice daga gidan.
“Tun da yanzu ta auri wani kuma diyata ba ta jin dadi a can, ta zabi zaunawa tare da ni da ‘yan uwanta.
“Ban sace ta ba, kawai na aiwatar da hukuncin kotuna da na Hukumar Shari’a, kuma yanzu tana makarantar kwana.”

- Nuhu Zaki

Kwamishina ya yaba wa mahaifin matarsa

Kwamishinan ya yaba wa mahaifinta marigayi Manu Soro da wasu da suka kokarta daidaita aurensu, amma wasu daga cikin iyalinta suka hana hakan.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya tona asirin yadda suka dauki hayan mata domin kifar da Jonathan

Nuhu Zaki ya ce kotuna uku sun ba shi nasara, amma har yanzu ana hana shi ganin diyarsa, duk da cewa mahaifiyarta ta sake yin aure.

Kwamishinan ya ce yana da niyyar kare ‘ya’yansa bisa doka da tsarin addini, yana mai bukatar dangin matar su daina korafin banza, cewar The Guardian.

An zargi kwamishina da lalata

A baya, mun ba ku labarin cewa Hukumar Hisbah a jihar Kano ta cafke wani kwamishina kan zargin lalata da matar aure.

Rahoto ya ce Kwamishinan da ake zargi ya fito daga jihar Jigawa inda ya shige da wata matar aure cikin wani kango mallakinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel