Gwamnan Bauchi ya nada Aliyu Tilde, Ladan Salihu, Aminu Gamawa mukamin kwamishinoni

Gwamnan Bauchi ya nada Aliyu Tilde, Ladan Salihu, Aminu Gamawa mukamin kwamishinoni

Gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya aika da sunayen mutane 20 da yake muradin nadawa mukamin kwamishinoni a sabuwar gwamnatinsa, gaban majalisar dokokin jahar domin ta tantancesu.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito kowacce karamar hukuma daga cikin kananan hukumomin jahar Bauchi 20 ta samu wakilci a cikin jerin sunayen da gwamnan ya aika ma majalisar, daga ciki har tsohon daraktan gidan rediyon Najeriya, Ladan Salihu.

KU KARANTA: Rikicin kabilanci: Gwamnatin jahar taraba ta sanya dokar hana shige da fice

Ga dai jerin sunayen kwamishinonin da kananan hukumomind a zasu wakilta, kamar haka:

Dakta Ladan Salihu, karamar hukumar Bauchi

Farfesa Adamu Ahmad, karamar hukumar Ningi

Samaila Burga, karamar hukumar Tafawa Balewa

Abdulrazak Nuhu Zaki, karamar hukumar Warji

Nura Manu Soro, karamar hukumar Ganjuwa

Auwal Jatau, karamar hukumar Zaki

Muhammad Sadiq, karamar hukumar Dass

Abdulkadir Muhd Chika Soro, karamar hukumar Alkaleri

Hajiya Hajara, karamar hukumar Itas/Gadau

Turaki Muhammad Manga, karamar hukumar Misau

Jidauna Tula Mbami, karamar hukumar Bogoro

Sarki Aliyu Jalam, karamar hukumar Dambam

Umar Abubakar Sade, karamar hukumar Darazo

Aminu Hassan, karamar hukumar Gamawa

Usman Muhammad, karamar hukumar Giade

Moddibo Abdulkadir, karamar hukumar Jama’are

Alhaji Umaru Adamu, karamar hukumar Katagum

Yakubu Bello Kirfi, karamar hukumar Kirfi

Hamisu M. Shira, karamar hukumar Shira

Aliyu Tilde, karamar hukumar Toro

Ana sa ran majalisar dokokin jahar Bauchi za ta tantance sunayen nan bada jimawa don baiwa gwamnan daman rantsar dasu a matsayin sabbin kwamishinonin gwamnatin jahar Bauchi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng