Daga Dawowa Najeriya, Tinubu Ya Gwangwaje Abba da Mukamin Shugaban Hukumar REA

Daga Dawowa Najeriya, Tinubu Ya Gwangwaje Abba da Mukamin Shugaban Hukumar REA

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Abba Abubakar Aliyu a matsayin shugaban hukumar REA bayan dawowarsa Najeriya daga Tanzania
  • Abba ya kasance mukaddashin shugaban REA tun daga Maris 2024, kuma zai shafe shekaru hudu a kan wannan mukami
  • Tinubu na fatan Abba zai yi amfani da kwarewarsa wajen samar da wutar lantarki a karkara don cimma muradun 'Renewed Hope'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Abba Abubakar Aliyu a matsayin shugaban hukumar wutar lantarki ta karkara (REA).

Nadin Abba na zuwa ne awanni bayan da shugaban kasar ya dawo Najeriya daga taron makamashi da ya halarta a kasar Tanzania.

Fadar shugaban kasa ta yi magana kan dalilin nada Abba Aliyu a matsayin shugaban REA
Tinubu ya amince da nadin Abba Aliyu a matsayin shugaban hukumar REA. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya nada Abba a mukamin shugaban REA

Bayo Onanuga, mai magana da yawun Tinubu ya fitar da sanarwar nadin a ranar Juma'a, 31 ga Janairu wadda Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu ta ba da mamaki a Kwara, ta fita a mota ta tattauna da dalibai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Bayo Onanuga ta nuna cewa Abba Abubakar Aliyu zai shafe shekaru hudu a kan wannan kujera, kuma nadin ya fara aiki daga 23 ga Janairun 2025.

Rahoto ya nuna cewa Abba ya kasance mukaddashin shugaban hukumar REA tun daga watan Maris din 2024 har zuwa lokacin nadin nasa.

Yadda Tinubu ya tsige tsohon shugaban REA

Idan ba a manta ba, a ranar 7 ga watan Maris din 2024, Legit Hausa ta rahoto cewa shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shugaban REA, Ahmad Salihijo Ahmad.

A lokacin, an ji cewa shugaba Tinubu ya dakatar da Ahmad tare da wasu manyan daraktocin hukumar zargin karkatar da kimanin Naira biliyan 2.1.

Bayan dakatar da Ahmad Salihijo, shugaban kasar ya kuma sa hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike kan yadda N2.1bn ta sulale a kan idonsa.

Dalilin Tinubu na nada Abba shugaban REA

A sabon nadin shugaban hukumar REA, Bayo Onanuga ya ce sabon shugaban, Abba yana da kwarewar shekaru 20 a harkar makamashi da ci gaban hukuma.

Kara karanta wannan

A karshe, an samu labarin rashin lafiyar da Tinubu ke fama da ita kafin zama shugaban ƙasa

"Ya taka muhimmiyar rawa a fannonin wutar lantarkin kasar nan da kuma alkinta albarkatun ruwa da na fannin zirga-zirga, wanda ya bunkasa tattalina rzikin Najeriya.
"Kafin nadinsa, shi ne shugaban sashen kula da ayyuka na shirin samar da wutar lantarkin Najeriya; babban manajan ayyukan hukumar, da kuma mataimakin shugaban kamfanin NBET."

- Bayo Onanuga.

Shugaba Bola Tinubu yana fatan Abba zai yi amfani da kwarewarsa wajen daga darajar REA da kuma samar da wutar lantarki a karkara da cimma muradun Renewed Hope kan makamashi.

EFCC ta gurfanar da daraktan REA

A wani labarin, mun ruwaito cewa, EFCC ta gurfanar da Sulaiman Bulkwang, daraktan kula da harkokin ma’aikata na REA, bisa zargin safarar kudaden haram da satar N223,412,909.

Sai dai Bulkwang ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa yayin da kotu ta ba da ajiyarsa a gidan yari zuwa ranar 3 ga Fabrairun 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel