Buhari ya nada Salihijo a matsayin shugaban REA kwanaki kadan bayan dakatar da Ogunbiyi

Buhari ya nada Salihijo a matsayin shugaban REA kwanaki kadan bayan dakatar da Ogunbiyi

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Ahmad Salihijo Ahmad a matsayin shugaban Hukumar samar da wutan lantarki a karkara (REA).

A ranar 24 ga watan Disamba ne ministan makamashi, Sale Mamman ya bayar da umurnin dakatar da Damilola Ogunbiyi daga mukaminsa na shugaban REA.

Ministan ya kuma bayar da umurnin gudanar da bincike kan zargin karya dokokin aiki da ake zargi hukumar ta yi karkashin jagorancin Ogunbiyi.

Mamman ya ce an dauki matakin ne don tsaftace ayyukan hukumar tare da inganta ayyukanta don samar wa al'umma ayyukan da ya dace.

DUBA WANNAN: Yadda wata amarya ta daure fuska a hoton auren ta ya dauki hankalin mutane

Sanarwar da mai magana da yawun ministan, Aaron Artmas ya fitar a ranar Talata a Abuja ya ce sabon shugaban na REA yana da ilimi da kwarewa sosai a bangaren na makamashi.

Ya ce Ahmad kwararre na a fanin samar da makamashi mai dorewa da ke da digiri na biyu a fanoni biyu da suka hada da ayyukan cigaba da tsare-tsaren ayyuka.

Ya kuma ce shugaban kasar ya nada Olaniyi Netufo a matsayin shugabna REA na sashin Kudu maso Yamma.

An kafa REA ne don inganta samar da wutar lantarki a karkakara da kauyuka ta hanyar kirkirar tsare-tsaren samar da lantarki da ba su dogara ga matattaran lantarki na kasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel