Kano: Rundunar 'Yan Sanda Ta Kama Masu Shirin Tayar da Bam a Maulidin Tijjaniya
- Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da alaka da dan ta’addan Chadi, Ahmad Adam Abba
- Ana zargin mutumin da kitsa kai hari taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyas da aka gudanar a Kano bayan kisan wasu a kasarsa
- Kwamishinan ‘yan sanda, Salman Garba Dogo, ya ce ana farautar Ahmad Adam Abba, wanda ya tsere daga Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane, ciki har da matar wani da ake zargin dan ta’addan Chadi ne mai suna Ahmad Adam Abba.
Ana zargin Abba da kitsa kisan mutane 17 a kasarsa ta haihuwa, sannan ya lallabo zuwa Najeriya domin kai hari a wajen taron tijjaniya a Kano.

Asali: Facebook
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya wallafa haka a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Salman Garba Dogo ya ce an kama wadannan mutane ne a jajibirin bikin Mauludin Tijjaniyya da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha.
‘Yan sanda na neman dan Chadi
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama wasu mutane uku da ke da alaka da wanda ake zargi, ciki har da matarsa da wani dan Chadi mai suna Jibrin Muhammed.
Kwamishinan ya ce:
“A yayin bincike, mun gano wasu abubuwan fashewa (IEDs), kuma muna ci gaba da gudanar da bincike.
"Wanda ake nema ya tsere daga Najeriya, amma mun samu nasarar cafke abokan aikinsa guda uku, ciki har da matarsa.”
Ya kara da cewa an kama mutanen ne ta hanyar bincike mai zurfi da kuma aiki bisa bayanan sirri, kuma a halin yanzu suna tsare yayin da ake ci gaba da bincike.
"Yan sanda su na aiki," Kwamishina
Kwamishinan ‘yan sanda, Salman Garba, ya yaba wa jami’ansa bisa kokarin da suka yi wajen cafke wadannan mutane.
A cewarsa:
“Muna aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro da jama’a domin gano duk wani aiki ko mutum da ke barazana ga tsaron kasa.”
Garba ya kara da cewa ana kara karfafa sintiri da sa ido a wuraren da ake ganin suna da hadari ga tsaro.
Haka kuma rundunar ta ce za ta ci gaba da wayar da kan jama’a domin su rika bayar da bayanai kan duk wani abu da ake zargin yana barazana ga zaman lafiya.
Yan sanda sun yi gargadin kai hari Kano
A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sandan Kano ta sanar da yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a sassan jihar, bayan samun rahoton sirri kan wasu ‘yan ta’adda.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya gargadi mazauna Kano da su guji wuraren da ke da cunkoso, ya ce an baza jami'ai domin dakile shirin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng