Rikicin Jam'iyya: Jagora a PDP Ya Ja Kunnen Atiku Abubakar da Nyesom Wike

Rikicin Jam'iyya: Jagora a PDP Ya Ja Kunnen Atiku Abubakar da Nyesom Wike

  • An zargi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Ministan Abuja, Nyesom Wike, da haddasa rikicin da ke ci gaba da rarraba jam'iyyar PDP
  • Kusa a jam'iyyar, Cif Bode George, PDP ya ce ya kamata ta duba cikin gida domin warware matsalolin da su ka haddasa mata rikicin da ake fama da shi
  • Cif George ya yi kira ga kafa kwamitin bincike kan rikicin PDP, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifi, dole a hukunta shi domin tabbatar da bin doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Cif Bode George, wani babban jagoran jam’iyyar PDP kuma memba na Hukumar Gudanarwar jam’iyyar, ya caccaki kusoshin jam'iyyar.

Ya danganta tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Ministan Abuja, Nyesom Wike, da rikicin saboda son kai, wanda ke kara jefa jam'iyyar a cikin rudani.

Kara karanta wannan

Bayan ba hammata iska a taron PDP, Sanata ya gaji da lamarinta, ya tuba zuwa APC

Atiku
Jigo a PDP ya nemi a sasanta rikicin jam'iyya Hoto: Nyesom Wike/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard News ta ruwaito cewa Cif George ya bayyana rikicin PDP a matsayin abin damuwa, inda ya ce ta na fuskantar rarrabuwar kai saboda son rai na kusoshin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kusa a PDP ya fadi silar rikicin PDP

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Cif George ya danganta asalin rikicin jam’iyyar PDP da taron jam'iyyar na kasa wanda aka yi kafin zaben shugaban kasa na 2023.

Ya nemi Atiku da Wike su daina wannan 'shirmen', ya na mai jaddada cewa ya kamata jam’iyyar ta duba abin da ke kara rikita ta a maimakon zargin APC da jawo mata matsala.

Jagora a jam'iyyar PDP ya nemi a sasanta

A bayaninsa, Cif George ya bukaci shugabannin PDP su kafa kwamitin bincike kan lamarin tare da daukar matakin hukunci ga duk wanda ya aikata laifi.

Ya ce:

“Rikicin da ake yi da APC ba zai taimaka mana ba. Dole ne mu zauna tare, duka bangarorin rikicin. Dukkan Atiku da Wike sun yi babban kuskure, kuma dole ne mu tashi da karfin gwiwa mu faɗa masu cewa ba za mu lamunci wannan ba.

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi?: Atiku ya ki halartar taron manyan kusoshin PDP da aka yi a Bauchi

“Ya kamata mu kafa kwamitin da zai binciki rikicin da ya fara tun daga lokacin taron jam'iyya, kuma mu warware shi.
Duk wanda aka samu da laifi mai tsanani, dole a hukunta shi. Wannan ba batu na kashin kai ba ne, kuma ba mu da uzuri; idan kai mamba ne na wata kungiya, akwai dokoki da ka'idoji da ya kamata ka bi.
Idan ba za ka iya bin dokokin ba, kuma ka yi tunanin za ka iya canza A zuwa B domin samun ci gaba, to, za mu cire ka."

PDP ta gudanar da babban taro

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta shirya gudanar da taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairun 2024 a daidai lokacin da ake ci gaba da rigima a cikinta.

Taron NEC na PDP yana da muhimmanci saboda yana ɗauke da damar warware matsalolin da ke rarraba jam'iyyar, musamman tsakanin waɗanda ke goyon bayan Atiku da waɗanda ke goyon bayan Wike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.