Jinkiri Ya Kare: Gwamnati Ta Fadi Watan da Matasa Ƴan NYSC Za Su Fara Karbar N77000

Jinkiri Ya Kare: Gwamnati Ta Fadi Watan da Matasa Ƴan NYSC Za Su Fara Karbar N77000

  • NYSC ta sanar da karin alawus ga matasa masu yiwa kasa hidima daga zuwa N77,000, kuma za su fara karɓa daga Fabrairun 2025
  • Gwamnatin tarayya ce ta amince da karin alawus din, inda shugaban NYSC ya bukaci matasan su nuna godiya ta hanyar aiki tukuru
  • Wasu matasa masu yiwa kasa hidima da Legit Hausa ta tattauna da su, sun nuna matukar jin dadi kan wannan albishirin na NYSC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban hukumar NYSC, Birgediya-Janar Yushau Ahmed, ya sanar da karin albashin matasa masu yiwa hidima zuwa N77,000.

Birgediya-Janar Yusha'u ya sanar da cewa matasa masu yiwa kasa hidima za su fara karbar sabon albashin ne daga watan Fabrairu 2025.

NYSC ta yi magana kan lokacin fara biyan sabon alawus din N77,000 ga matasa masu yiwa kasa hidima
Gwamnatin Tinubu za ta fara biyan matasa masu yiwa kasa hidima N77000 daga Fabrairu. Hoto: @officialABAT, @officialnyscng
Asali: Twitter

An sanya ranar karawa 'yan NYSC alawus

Yayin da yake jawabi ga matasan na 2024 Batch ‘C’ Stream II a Katsina, ya bayyana cewa an sanya karin albashin nasu a cikin kasafin kudin 2025, inji rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Magana ta zo karshe: Shugaban NYSC ya fadi lokacin fara biyan N77,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Birgediya-Janar Yusha'u ya ce watan Janairu ya riga ya kare, amma da zarar an amince da kasafin kudin, za su fara karbar N77,000 maimakon N33,000 da ake biya.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ce ta amince da karin kudin, don haka ya bukaci matasan su nuna godiya ta hanyar yin aiki tukuru.

NYSC ta ba da tabbacin kula da masu hidima

Shugaban hukumar da ke kula da matasa masu yiwa kasa hidimar ya jaddada cewa yana da burin tabbatar da jin daɗi da tsaron 'yan bautar kasar.

Jaridar ThisDay ta rahoto Birgediya-Janar Yusha'u ya tabbatar da cewa ba za a tura matasa zuwa yankunan da ke fama da matsalar tsaro don yin bautar kasa ba.

Ya ce duk inda matasan suka ga an tura su, to su kwantar da hankulansu domin sai hukumar ta gamsu da tsaron wuri take tura masu yiwa kasa hidima.

NYSC: Matasa sun yiwa gwamnati godiya

Kara karanta wannan

'Da yanzu abinci ya gagari talaka': Yadda CBN ya ceto tattalin Najeriya a 2024

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu matasa masu yiwa kasa hidima kan wannan albishir da Birgediya-Janar Yusha'u ya yi na fara biyansu sabon alawus.

Hauwa'u Lawal Mailafiya da ke bautar kasa a jihar Katsina ta ce:

"Mun ji dadi sosai, dama mun dade muna korafi kan jinkirin fara biyan kudin. Amma ni ba zan wani amfana sosai ba, saboda bai wuce wata biyar ya rage na kammala ba.
"Duk da haka, muna godiya ga gwamnati da ta cika alkawarin, ko ba komai za mu samu wadatattun kudin da za mu ci gaba da gudanar da bautar kasa cikin kwanciyar hankali."

Wata kawar Hauwa'u, wadda suke yin bautar kasa tare, mai suna Zainab Yahaya Bature ta ce:

"Ni kamar na fi kowa farin ciki domin karin da aka yi zai ba ni damar fara sana'ar da na dade ina so na yi."

Ko da wakilin Legit Hausa ya tambayeta sana'ar da take son yi, sai cewa ta yi:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

"Yin awara ina sayarwa a soshiyal midiya. Ba abin dariya ba ne, saboda na taba yi kuma na samu riba. Maimakon in zauna idan mun dawo daga PPA, gwanda na dora kasko a cikin gida in rika soya awara ina sayarwa.
"Na san cewa 'yan anguwar da nake za su saya, wadanda muke bautar kasa tare da su da ke kusa da gidan da muke za su saya, sannan 'yan soshiyal midiya da ke a garin za su saya."

Dalilin jinkirin fara biyan 'yan NYSC N77,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban hukumar NYSC, Birgediya-Janar Yushau Ahmed ya ce gwamnati ba ta sakar masu kudin fara biyan matasa N77,000 ba.

Birgediya-Janar Yushau duk da cewa gwamnati ta amince da karin alawus din, matasa masu yiwa kasa hidima za su fara ganin karin idan an saki kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel