Sarki Ya Aikawa Sarkin Musulmi Wasika, An Fada Masa Illar Kafa Shari'ar Musulunci a Kudu

Sarki Ya Aikawa Sarkin Musulmi Wasika, An Fada Masa Illar Kafa Shari'ar Musulunci a Kudu

  • Oba Omo Tooyosi Akinleye ya bayyana rashin dacewar kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma, ya ce hakan zai haddasa rikici
  • Basaraken ya jaddada cewa tsarin dimokuradiyya ya fi dacewa, domin yana bai wa kowa 'yancin addini ba tare da fifita wata akida ba
  • Ya bukaci sarkin Musulmi da ya yi nazari kan lamarin, domin a kiyaye tsarin da zai kare zaman lafiya da kuma hadin kan al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - Sarkin Ilukosi-Ijesa na Yarbawa, Oba OmoTooyosi Adebayo M. Akinleye ya yi magana kan takaddamar da ake yi na kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma.

Oba OmoTooyosi ya goyi bayan masu adawa da kafa shari'ar Musulunci a yankin Yarbawa, yana mai cewa hakan zai haifar da rashin zaman lafiya.

Sarkin Ilukosi-Ijesa ya aika wa sarkin Musulmi wasika kan takaddamar kafa shari'ar Musulunci a Kudu
Basaraken Yarbawa ya fadawa sarkin Musulmi illar kafa shari'ar Musulunci a Kudu. Hoto: @letsbuildnew9ja
Asali: Twitter

Sarkin Ilukosi-Ijesa ya bayyana haka a wasikar da ya aikawa sarkin Musulmi, Mai alfarma Sa'ad Abubakar ta shafinsa na X a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Sun watse mana': Atiku ya fadi abin da yan Najeriya suka yi musu yayin kamfen siyasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauyin tsarin shari'a a jihohin Yarbawa

Oba OmoTooyosi ya shaidawa sarkin Musulmi cewa tun da fari, tsarin shari'a na Osugbo/Ogboni ya taka muhimmiyar rawa a matsayin babbar kotu ga Yarbawa.

A hankali, al'ummar Yarbawa suka koma kan tsarin shari'a na zamani, tare da rungumar dokokin da ke ba kowa 'yancin addini da tsarin rayuwa.

Basaraken ya ce wannan sauyin ya bai wa mutane damar samun adalci ba tare da dogaro da wata al'ada ko addini ba, wanda hakan ke kare hakkin kowa.

"Matsalar kafa shari'ar Musulunci" - Sarkin Ilukosi-Ijesa

Oba OmoTooyosi ya yi magana kan batun kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma, yana jaddada cewa Najeriya kasa ce mai bin tsarin dokar kasa.

Ya yi gargadin cewa aiwatar da shari'ar Musulunci a yankin zai iya haddasa sabani, musamman tsakanin Kiristoci da masu bin al'adun gargajiya.

A cikin wasikar, basaraken, ya shaidawa sarkin Musulmi cewa:

"Dangane da dokar sharia a Kudu maso Yamma, aiwatar da ita zai haifar da kalubale saboda tsarinmu na dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya tona asirin yadda suka dauki hayan mata domin kifar da Jonathan

"Najeriya kasace da ke tafiya a kan tsarin dimokuradiyya inda babu wani addini da aka amince ya zama addini kasar, wanda hakan ke ba kowa damar yin addinin da ya so ba tare da takura ba.
"Shigo da tsarin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma zai gurgunta 'yanci, wanda zai haddasa tashin hankali tsakanin mabiya addinai da zamantakewa."

An roki Sarkin Musulmi ya duba batun a tsanake

Oba OmoTooyosi ya bayyana cewa tsarin dimokuradiyya ya kawo zaman lafiya da hadin kai, tare da bai wa kowa damar yin rayuwa cikin 'yanci.

Sarkin ya bukaci a kiyaye tsarin shari'a na Kudu maso Yamma, domin kada a bari wani addini ya rinjayi tafiyar da mulki ko shari'ar mutane.

"Misali, shari'ar Musulunci bai yi daidai da tsarin Kiristoci da mabiya addinin gargajiya ba, wanda zai haifar da rashin zaman lafiya.

- A cewar sarkin Ilukosi-Ijesa.

Ya roki sarkin Musulmi da ya yi nazari kan takaddamar da ake yi da kuma duba tsarin shari’ar gama-gari da ake yi a duniya wanda zai amfanar da dukkan Najeriya.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

A karshe, Oba Akinleye ya tabbatar da goyon bayansa ga tsarin shari'ar dimokuradiyya don tabbatar da adalci da kare hakkin kowa.

Ana takaddama kan kafa shari'ar Musulunci a Kudu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, takaddama mai zafi ta barke a shiyyar Kudu maso Yamma kan batun kafa kwamitocin shari'ar Musulunci.

Rigimar ta tsananta ne bayan an kafa kwamitin shair'ar a jihar Ekiti, inda basaraken jihar ya rusa shi, lamarin da ya jawo martani daga kungiyoyin Musulmai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel