Tsohon Shugaban APC Ya Fadi Rawar da Buhari Ya Taka a Sanya Osinbajo Takara da Tinubu
- Tsohon gwamnan jihar Osun kuma shugaba a jama'iyyar APC, Bisi Akande, ya taɓo batun samun tikitin APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
- Bisi Akande ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai so Farfesa Yemi Osinbajo ya yi takara da Bola Tinubu ba
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa shi ne ya ba da shawara aka naɗa Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari lokacin shiga zaɓen 2015
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande, ya yi magana game da rikicin siyasa da ake zargin akwai tsakanin Shugaba Bola Tinubu da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.
A yayin da ake shirin zaɓen 2023, Yemi Osinbajo, wanda a wancan lokaci yake matsayin mataimakin shugaban ƙasa, ya shiga takara a zaɓen fitar da gwanin APC da Tinubu da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

Asali: Twitter
Bisi Akande ya yi magana kan yadda ta kaya a wancan lokacin yayin hira da Edmund Obilo, wacce aka sanya a shafin Youtube.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yemi Osinbajo ya yi takara da Bola Tinubu
Takarar da Osinbajo ya fito a lokacin ta haifar da ƴar tsama tsakanin shi da Tinubu, wanda yake a matsayin ubangidansa bayan ya yi masa kwamishina na tsawon shekaru takwas yayin da yake gwamnan Legas.
Lamarin ya raba kan magoya bayan Tinubu, inda wasu kamar tsohon Sanata Babafemi Ojudu suka nuna goyon bayansu ga Osinbajo.
A yayin hirar, Bisi Akande ya bayyana cewa shi ne ya ba da shawarar a naɗa Osinbajo mataimakin shugaban ƙasa lokacin da suka tattauna da Tinubu kan batun maye gurbin Fasto Tunde Bakare.
Fasto Tunde Bakare shi ne abokin takarar Buhari a ƙarƙashin jam’iyyar CPC a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2011.
Shekaru huɗu bayan wannan zaɓen, Buhari ya sake yin takara tare da Osinbajo a matsayin mataimakinsa, suka samu nasarar lashe zaɓe.

Kara karanta wannan
A karshe, an samu labarin rashin lafiyar da Tinubu ke fama da ita kafin zama shugaban ƙasa
Wace rawa Buhari ya taka a takarar Osinbajo
Da aka tambaye shi ko Buhari ya hana Tinubu tsayawa takara, Bisa Akande ya bayyana cewa ko kaɗan tsohon shugaban ƙasan bai yi hakan ba.
“Bai faɗa mani haka ba. Na yi masa tambayoyi da yawa, har da ko shi ne ya sanya Osinbajo ya tsaya takara da Tinubu."
"Sai ya ce a’a, ya kuma yi mani bayanin cewa, a al’adarsa, idan maigidanka yana son wani matsayi, ba za ka tsaya takara da shi ba."
- Bisi Akande
Tinubu ya haɗu da Osinbajo a ƙasar waje
A farkon makon nan, Osinbajo da Tinubu sun haɗu a wani taro kan makamashi da aka yi a ƙasar Tanzania. A yayin taro mutanen biyu sun gaisa sannan suka ɗauki hotuna tare.
Wannan haɗuwar dai ita ce ke zama ganawarsu ta farko a bainar jama’a tun bayan da Tinubu ya zama shugaban ƙasa a 2023.
Bisi Akande ya yi magana kan lafiyar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande, ya bayyana cewa Bola Tinubu ya yi masa ƙorafi kan rashin lafiyarsa kafin ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
A cewar tsohon gwamnan na jihar Osun, a wancan Shugaba Bola Tinubu yana fama da matsalar ciwon ƙafa wanda ya addabe shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng