'Da Yanzu Abinci Ya Gagari Talaka': Yadda CBN Ya Ceto Tattalin Najeriya a 2024
- Babban Bankin Najeriya ya ce da ba a yi amfani da manufofinsa ba, da hauhawar farashin kaya ya iya kai wa 42.81% a Disamba 2024
- CBN ya ce ya ƙara yawan kudaden da 'yan Najeriya ke tura wa daga kasashen waje zuwa $4.18bn cikin watanni uku na farkon 2024
- A wani taro a Abuja, gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya lissafa wasu dabaru da bankin ya yi amfani da su wajen daidaita tattali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban Bankin Najeriya ya ce da ba a yi amfani da dabarunsa ba, da hauhawar farashin kaya ya haura zuwa kashi 42.81% a Disambar 2024.
CBN ya kuma yi hasashen cewa kudaden da 'yan Najeriya ke tura wa daga kasashen waje za su tashi zuwa N31.79tn idan aka fitar da kididdigar zangon karshe na 2024.

Asali: Twitter
Jaridar The Nation ta rahoto cewa babban bankin ya yi alkawarin ci gaba da bin tsare-tsarensa na kudi don shawo kan hauhawar farashin kaya a 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CBN ya ceto Najeriya daga hauhawar farashi
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana wannan a ranar Alhamis a Abuja a taron Dokokin Manufofin Kudi na 2025.
Rahoto ya nuna cewa taron ya haɗa ministoci da shugabannin hukumomin tattalin arziki da masu zaman kansu.
"Rahoto ya nuna cewa da CBN bai dauki kwararan matakai ba, to da hauhawar farashin kaya ya kai kashi 42.81% a Disamba 2024," inji Cardoso.
Ya kuma bayyana cewa CBN ta aiwatar da tsare-tsare masu tsauri a manyan tarukan kwamitin manufofin kudi shida da aka gudanar a 2024.
Tsare-tsaren sun hada da kara yawan kudin MPR da maki 875 zuwa kashi 27.50%; kara kudin ajiyar CRR na sauran hukumomin ajiyar kudi (ODCs) da maki 1750 zuwa kashi 50%.
Tsare tsaren da CBN ya bullo da su a 2024
Cardoso ya lissafa wasu daga cikin muhimman tsare-tsaren da CBN ya aiwatar domin yin garambawul ga musayar kudaden waje da inganta hada-hadar kudi.
CBN ya ce matakin daidaita kasuwar musayar kudi ya sa an samu hada hadar kudi a tsakanin IMTO da ya kai $4.18bn a zango uku na 2024, wanda ya zarce $2.33bn da aka samu a 2023.
Jaridar Punch ta rahoto sauran tsare-tsaren na CBN sun hada da biyan bashin $7bn wanda ya dawo da darajar kasuwar da kara yawan kudaden da ake hada hadarsu.
Babban bankin ya ce ya kuma kaddamar da tsarin WIFI karkashin tsarin kudi na kasa da zai cike gibin samuwar kudi ga kowa, inda aka tallafawa mata da ilimi, kayan aiki da kudi.
Hakazalika, CBN ya bullo da tsarin musayar kudi na kasashen waje na Najeriya (NFEC) domin tabbatar da yarda, aminci da nagartar kasuwannin musayar kudi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
Bankin CBN ya gano masu jawo karancin kudi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ci tarar bankuna tara Naira biliyan 1.35 saboda gazawar su wajen fitar da takardun kudi ta ATM.
Rahotanni sun nuna cewa kowane bankin da aka samu da laifi an ci tararsa Naira miliyan 150 saboda karya dokokin rarraba kudi na CBN.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng