FIRS Ta Tashi kan Tinubu, Ta Fadi Tiriliyoyin da Najeriya Ta Samu Daga Haraji a 2023

FIRS Ta Tashi kan Tinubu, Ta Fadi Tiriliyoyin da Najeriya Ta Samu Daga Haraji a 2023

  • Hukumar FIRS ta samu nasarar tattara harajin Naira tiriliyan 21.6 a 2024, wanda ya zarce Naira tiriliyan 19.4 da ta yi burin tarawa
  • Shugaban FIRS, Dakta Zacch Adedeji, ya ce hukumar tana shirin tara naira tiriliyan 25.2 a 2025 ta hanyar amfani da fasahar zamani
  • Hukumar ta fadi matakan da ta dauka domin tatso Naira tiriliyan 25.2 daga 'yan Najeriya na haraji a shekarar nan da muke ciki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) ta bayyana cewa ta zarce burinta na tara Naira tiriliyan 19.4 na kudaden shiga a 2024, inda ta tara Naira tiriliyan 21.6.

Shugaban FIRS, Dakta Zacch Adedeji, ya bayyana hakan ne yayin taron fayyace dabarun gudanarwar hukumar na 2025 da aka shirya a Abuja a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Da yanzu abinci ya gagari talaka': Yadda CBN ya ceto tattalin Najeriya a 2024

Shugaban hukumar FIRS ya fadi adadin tiriliyoyin da gwamnatin Najeriya ta samu na haraji a 2024
Hukumar FIRS na shirin tara Naira tiriliyan 25 na haraji a 2025 da ta tara N21.6trn a 2024. Hoto: @FIRSNigeria
Asali: Facebook

FIRS ta tara N25.2trn na haraji a 2024

Shugaban FIRS ya ce hukumar na da burin tatso Naira tiriliyan 25.2 na haraji a shekarar 2025, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Adedeji ya ce hukumar ta cimma gagarumar nasara a 2024 wadda za ta dade a cikin tarihin FIRS, bayan ta tara harajin Naira tiriliyan 21.6.

Ya ce Naira tiriliyan 21.6 da hukumar ta tara ya zarce Naira tiriliyan 19.4 da ta yi burin tarawa tun da farko, kuma ta cimma nasarar ta hanyar jajircewa da ingantaccen tsari.

FIRS ta dauki sababbin dabarun tara haraji

Shugaban ya ce nasarar hukumar ta biyo bayan amfani da dabarun shugabanci, kwazon ma’aikata, fasahar zamani da kyakkyawan tsarin gudanarwa.

"Aikin FIRS yana ba gwamnati damar gina manyan tituna, samar da ayyukan jin dadin jama’a da kuma hanyoyin da ke inganta rayuwar mutane," inji Dakta Adedeji.

Ya ce ma’aikatan FIRS ba kawai ma’aikata ba ne, a’a, suna da alhakin hidimtawa kasa wajen tabbatar da ci gaba da bunkasar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Ana maganar kudirin haraji, Naira ta sake farfaɗowa bayan sababbin matakan CBN

FIRS na son tara harajin N25trn a 2025

Game da burin hukumar a 2025, Dakta Adedeji ya ce za su mai da hankali kan inganta ayyuka domin samar da ci gaba na dogon zango.

Ya ce fasahar zamani za ta taka muhimmiyar rawa wajen saukaka tsarin biyan haraji da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi.

A cewarsa, FIRS za ta fadada tsarin hada-hadar haraji ta amfani da fasaha, wanda zai bunkasa karbar kudaden haraji daga 'yan kasuwa da kamfanoni.

Dakta Adedeji ya ce bayan nasarar FIRS a shekarar 2024, a yanzu hukumar tana shirin cimma burin tara Naira tiriliyan 25.2 a 2025.

Hukumar FIRS ta tara Naira tiriliyan 12.3 a 2023

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar FIRS ta ce kudaden harajin da ta tattara a shekarar 2023 sun haura Naira Tiriliyan 12.3.

Shugaban hukumar, Dakta Zacch Adedeji, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai kasuwar duniya da ke Enugu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.