An Shiga Alhini, Sarkin Fadar Zazzau Ya Koma ga Mahalicci Ana cikin Taro
- Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, Sarkin Yakin Zazzau, ya rasu a safiyar Alhamis, 30 Janairu, 2025 ana tsaka da taro a wani asibiti
- Za a yi jana'izar marigayin a gidansa dake Rimin Doko, Unguwar Kaura, a Birnin Zariya, tare da gudanar da sallah a misalin karfe 5:00
- Majiyar Legit Hausa ta tabbatar da cewa ai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya fito domin a sallaci marigayin.'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Masarautar Zazzau ta shiga alhini bayan rasuwar Sarkin Yakin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate.
Masarautar ta sanar da rasuwar ne a safiyar ranar Alhamis, 30 Janairu, 2025, inda ta bayyana cewa Alhaji Pate ya rasu ne ana tsaka da taro.

Asali: Facebook
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Sarkin Yakin ya rasu a wajen wani taro da ke gudana a asibitin Gambo Sawabo a safiyar yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a yi wa Sarkin Yakin Zazzau sutura
Masarautar Zazzau ta bayyana cewa za a yi jana’izar Alhaji Rilwani Yahaya Pate a gidansa da ke Rimin Doko, Unguwar Kaura, cikin Birnin Zariya.
Malam Safyan Bammali, guda ne daga mazauna masarautar Zazzau, ya kuma shaida wa Legit cewa an sanya za a yi masa sallah da misalin 5:00 na yamma.
Da ya ke amsa kiranmu da misalin 4:52, ya shaida cewa yanzun nan Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya fito domin a sallaci marigayin.
Ya kara da cewa jama'a sun riga sun hallara, ana jiran Mai Martaba Sarki ya kimtsa domin a yi wa Alhaji Pate sallah, inda daga bisani a raka shi makarbarta kamar yadda Musulunci ya yi umarni.

Kara karanta wannan
"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe
Uwar gidar Shehun Zazzau ta rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah Ya karbi rayuwar Hajiya Habiba Shehu Idris, uwar gidar marigayi Shehu Idris, Sarkin Zazzau na 18, a safiyar ranar Juma'a, 30 Agusta, 2024.
Masarautar Zazzau tabayyana cewa, Hajiya Habiba ta rasu bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya, kuma ta kara da bayyana cewa rasuwarta ta kawo babban alhini ga masarautar da al'ummar Zazzau.
Hajiya Habiba, ta kasance uwar gidar marigayi Dakta Shehu Idris, wanda ya jagoranci masarautar Zazzau na tsawon shekaru, kuma tana daga cikin manyan mata masu tasiri a cikin al'ummar Fulani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng