"Najeriya ba Ta IMF ba ce," Gwamnan Adamawa Ya Soki Tsarin Tattalin Arzikin Tinubu

"Najeriya ba Ta IMF ba ce," Gwamnan Adamawa Ya Soki Tsarin Tattalin Arzikin Tinubu

  • Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na Adamawa ya bi sahun takwaransa na Bauchi wajen sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya
  • Fintiri ya shawarci gwamnatin tarayya da ta sauya alkiblar manufofinta domin saukaka wa ‘yan Najeriya wahalhalun da su ke fuskanta
  • Ya bukaci Tinubu da ya fahimci cewa Najeriya ce ya ke jagoranta, ba Bankin ba da Lamuni na Duniya (IMF) ko kuwa Bankin Duniya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri ya bi sahun takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed a wajen sukar manufofin gwamnatin APC, karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan ya na ganin yadda Shugaban kasa, Tinubu ya bijiro da manufofin tattalin arziki ba su dace da yanayin da ‘yan Najeriya su ke ciki ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

Finitir
Gwamnan Adamawa ya soki tsarin tattalin arzikin Tinubu Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

AIT News ta wallafa cewa Ahmadu Fintiri ya shawarci gwamnatin tarayya a kan abubuwan da su ka dace da tattalin arzikin Najeriya, matukar da gaske ake bukatar dawo da Najeriya cikin hayyacinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Adamawa ya shawarci Tinubu

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Finitiri ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed da ya san cewa Najeriya ya ke jagoranta, ba Bankin ba da lamuni na duniya (IMF) ko Bankin Duniya.

Ya ce akwai bukatar shugaban kasar ya gaggauta sauya akalar tattalin arzikinsa zuwa abin da zai ciccibo ‘yan Najeriya daga halin matsin rayuwa da su ke fuskanta sakamakon manufofinsa.

A ina gwamnan Adamawa ya shawarci Tinubu?

Gwamnan Adamawa ya mika shawarwarinsa ga Shugaban Najeriya yayin taron PDP na neman hade kan ‘yan jam’iyya na Arewa maso Gabas da ya gudana a jihar Bauchi.

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da kansa ya sha nanata wa Bola Tinubu cewa manufofinsa ba sa tabuka komai, sai jefa jama’a a cikin karin matsi da karo matsalar hauhawar farashi.

Kara karanta wannan

'Ku nemi gafara': Bashir Ahmad ga masu sukan tikitin Musulmi da Musulmi, ya fadi dalilansa

Gwamnan Adamawa ya halarci taron PDP

Taron babbar jam’iyyar hamayya da ke gudana a jihar Bauchi na kokarin hade kan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da ke fuskantar baraka, da sauran matsalolin shugabanci da ke damun jam’iyyar gabanin zaben 2027.

Wadanda su ka halarci taron sun hada da Shugaban PDP na PDP na riko, Umar Iliya Damagum da Shugaban gwamnonin PDP, Bala Mohammed.

Sauran sun hada da Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba, sai kuma shugaban kwamitin sasanta kan ‘yan jam’iyyar PDP da sauransa.

Zuwa lokacin hada wannan labari, kusoshin PDP sun shiga ganawar sirri domin lalubo bakin matsalar da ke kokarin durkusar da jam’iyyar a halin da ake ciki.

An gargadi Tinubu kan karuwar talauci

A wani labarin, mun wallafa cewa rahoton PricewaterhouseCoopers International Limited ya bayyana fargabar akalla mutane sama da miliyan 13, za su fada mummunan talauci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Abincin wasu ya kare: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 5, an maye gurbinsu nan take

Rahoton, wanda aka fitar da shi bayan dogon bincike ya bayyana cewa hakan za ta faru ne saboda hauhawar farashi da faduwar darajar Naira, inda aka shawarci Bola Tinubu ya dauki mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel