Jami'an Tsaro Sun Yi Bajinta, Sun Ragargaji 'Yan Bindiga da Masu Sace Mutane

Jami'an Tsaro Sun Yi Bajinta, Sun Ragargaji 'Yan Bindiga da Masu Sace Mutane

  • Jami'an tsaro na rundunar Agunechemba sun ƙaddamar da farmaki cikin tsakar dare kan maɓoyar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar Anambra
  • A yayin farmakin, jami'an tsaron tare da haɗin gwiwar sojoji da ƴan sanda sun samu nasarar sheƙe ƴan bindiga masu tarin yawa
  • Jami'an tsaron sun kuma ƙwato kayayyaki masu yawa daga hannun miyagun yayin da suka kuma cafke wani ɗan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Rundunar tsaro ta Agunechemba da gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo ya kafa, ta kai farmaki sansanin ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Jami'an rundunar tare da haɗin gwiwar sojoji da ƴan sanda sun kashe ƴan bindiga masu yawa a yayin farmakin.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a Anambra
Jami'an tsaro sun sheke 'yan bindiga masu yawa a Anambra Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu daga cikin miyagun sun tsere da raunuka daban-daban, yayin da aka ƙwato makamai da wasu kayayyaki daga hannunsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban karamar hukuma a Katsina, sun yi barna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro sun ragargaji ƴan bindiga

Tun bayan ƙaddamar da rundunar wacce ke kama da tsohuwar rundunar "Bakassi Boys" da aka samar a zamanin tsohon gwamna Chinwoke Mbadinuju, ta ragargaza sansanin ƴan bindiga guda shida a jihar.

Rundunar ta kai farmakin ne a garin Enugu-Agidi, cikin ƙaramar hukumar Njikoka, da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Laraba.

Dakarun rundunar tare da haɗin gwiwar ƴan sanda, DSS, sojoji da sauran jami’an tsaro ne suka ƙaddamar da farmakin.

Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri, sannan an kama ɗaya daga cikin ƴan bindigan.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogin AK-47 guda biyu, manyan bindigogi guda takwas, ƙananan bindigogi guda huɗu da harsasai guda 101.

Sauran sun haɗa da jigida guda huɗu na AK-47, adduna guda uku, rediyon Baofeng guda ɗaya, babur guda ɗaya da layuka masu yawa.

Ƴan sanda sun ce wani abin kan lamarin

Kara karanta wannan

'Yan sa kai sun yi ta'asa a Neja, 'yan sanda sun yi caraf da su

Ba a samun jin ta bakin kakakin ƴan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ba domin ƙarin bayani kan lamarin.

Sai dai daya daga cikin manyan jami’an ƴan sanda a jihar ya tabbatar da afkuwar farmakin.

"Wannan aikin haɗin gwiwa ne da aka gudanar bayan tattara bayanan sirri. Gwamna Soludo ya bada umarni a tabbatar da tsaron jihar Anambra, kuma mun kuduri aniyar ganin mun kawo ƙarshen waɗannan miyagun."

- Babban jami'in ɗan sanda

Sojoji sun kashe shugaban ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe wani hatsabibin shugaban ƴan ta'adda a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Kakakin hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa an kashe shugaban ƴan ta'addan ne a ƙaramar hukumar Barikim Ladi ta jihar Plateau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel