Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Bama Bamai kan 'Yan Boko Haram, Sun Soye Miyagu Masu Yawa
- Dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai sun ƙara azama a yaƙin da suke yi da ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
- Sojojin sun kai hare-haren bam a maɓoyar ƴan ta'addan Boko Haram da ke ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno
- Ruwan bama-baman da sojojin suka yi kan ƴan ta'addan ya yi sanadiyyar kashe miyagu masu yawa tare da jikkata wasu da dama
- Hare-haren dai babbar nasara ce a yaƙin da sojoji suke yi domin kawar da barazanar ƴan ta'addan Boko Haram da ke ta'adi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun sojojin saman Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai, sun kai hare-haren bam kan ƴan ta'addan Boko Haram a Borno.
Dakarun sojojin sun kashe ƴan Boko Haram masu yawa a farmakin sama da suka kai a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Asali: Getty Images
Jaridar The Punch ta rahoto cewa an kai hare-haren ne da nufin kawar da wasu shugabannin ƴan ta'addan na Boko Haram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin sama sun ragargaji ƴan Boko Haram
Bayanan sirri sun nuna cewa an shirya gagarumin taron ƴan Boko Haram a yankin da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Talata.
Hare-haren an kai su ne sansanonin ƴan ta’adda da ke ƙarƙashin ikon Ali Ngulde, wanda sanannen shugaban ƴan Boko Haram ne.
Wata majiya daga ɓangaren sojoji ta bayyana cewa an kashe ƴan ta'adda da dama, yayin da wasu suka samu munanan raunuka.
Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Jingina, domin samun ƙarin bayani kan sakamakon farmakin, ya ci tura.
Wannan farmakin wani babban ci gaba ne a yaƙi da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas, musamman ganin yadda aka kashe shugabannin Boko Haram da ke da matsayi mai girma.
Har yanzu dai bincike na ci gaba don tantance yawan ƴan ta’addan da aka kashe, tare da ƙimanta yadda harin ya shafi sansanonin su da kuma makaman da suka rasa.
Sojoji sun sheƙe ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan sansanonin ƴan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara.
Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga masu yawa a yayin harin bayan sun sakar musu bama-bamai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng