Rundunar Yan Sanda Ta Kori Kurtun da Ake Zargi da Karbar Rashawa a Titunan Kano
- Rundunar ‘yan sandan Kano ta kori wani kurtu mai suna Ado Abba bisa zargin karɓar cin hanci daga jama’a a kan titi
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce akwai ranar da ya taba fada wa komar Ado
- Ya nemi hadin kan mazauna Kano wajen kawo korafi a kan duk jami'in dan sandan da ake zargi da aikata ba dai-dai ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana korar wani kurtu, Ado Abba bayan korafe-korafen jama'a na zargin jami'in da karbar na goro a kan titi.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka, inda ya ce shi kan shi ya taba fadawa komar korarren jami'in a lokacin da ya ke tsaka da tafiya a motarsa.

Asali: Facebook
A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, SP Kiyawa ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan Kano, Salman Dogo ne ya yi umarnin a kori tsohon kurtun dan sandan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya tabbatar da cewa sai da rundunar ta gudanar da sahihin bincike a kan korafin da aka shigar a gabanta, kafin ta yanke hukuncin sallamar jami'in.
Rundunar 'yan sanda ta gargadi jami'anta
Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya jaddada cewa rundunar ta na bakin kokarinta domin tsaftace yadda ake gudanar da aikin dan sanda.
Ya nanata cewa rundunar ba za ta amince da duk wasu jami'ai da ke zargi da karbar cin hanci da rashawa a titunan jihar ba.
Kiyawa ya ce:
"Duk irin wadannan da su ke fakewa da kayan 'yan sanda su na cutar mutane, kar a yi shiru.
"Idan an ga wannan, ko irinsu da ku ke zargi, ba shiru za ku yi ba. Ku yi kokari ku sanar da mu a lambobinmu."
An samu masu taimakon korarren dan sanda
Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa an samu wani bawan Allah da ya yi alkawarin taimaka wa jami'in da aka kora bisa zargin karbar cin hanci.
SP Kiyawa ya wallafa cewa:
"Wani yayi alkawarin ba shi jari, sannan wani yayi alkawarin bashi aikin 'Kamfani. Allah ya sa haka yafi masa alkairi."
Rundunar 'yan sanda ta nemi dauki
'Yan sandan jihar Kano sun bayyana cewa aikin tsaro hakki ne da ya rataya a wuyan dukkanin 'yan kasa, saboda haka, akwai bukatar a rika taimakonsu da bayanan sirri.
Kakakin 'yan sandan ya ce:
"Mu na godiya da hadin kai da ake ba mu a kowane lokaci. Kuma, mu na kara jan hankalin al'umma, abin da ya shafi tsaro, ba na mu ne na 'yan sanda kadai ba da sauran jami'an tsaro. Abu ne da ya shafi al'umma baki daya."
Ana son samar da hukumar tsaro a Kano

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
A baya, mun ruwaito cewa majalisar dokokin Kano ta fara kokarin ba gwamnatin Abba Kabir Yusuf ikon samar da hukumar tsaro mallakin jihar domin taimaka wa wajen dakile rashin tsaro.
Ana sa ran ba hukumar ikon rike makamai, yin kame da kuma tsare duk wanda ake zargi da aikata laifuffuka gabanin mika shi hannun rundunar 'yan sandan kasar nan reshen jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng