Bayan Abin da Ya Faru a Filin Jirgin Kano, NCAA Ta Dakatar da Kamfanin Max Air
- Gwamnatin tarayya ta dakatar da harkokin sufurin kamfanin jiragen sama na Max Air na tsawon watanni uku a Najeriya
- Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasa (NCAA) ta ce an dakatar da kamfanin ne bayan abin da ya faru a Kano
- A ranar Talata da daddare, wani jirgin saman Max Air ya gamu da hatsari a lokacin sauka a filin jirgin Mallam Aminu Kano
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta hannun hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta dakatar da ayyukan jiragen Max Air na tsawon watanni uku.
Hukumar NCAA ta ɗauki wannan matakin ne bayan afkuwar wani lamari da ya shafi jirgin kamfanin a daren Talata a Kano.

Asali: Getty Images
Daily Trust ta kawo rahoton cewa Jirgin Max Air B734 mai lamba 5N-MBD ya fuskanci fashewar taya yayin sauka a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano.

Kara karanta wannan
Max Air ya fitar da bayanai a kan hatsarin jirginsa a Kano, an rufe titin saukar jirage
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hatsarin wanda ya afku ne a ranar Talata, 28 ga Janairu, 2025, da misalin karfe 10:51 na dare, shi ne na uku da jirgin kamfanin Max Air ya fuskanta a watanni uku.
NCAA ta dakatar da jiragen Max Air
Duk da cewa dukkan fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun tsira ba tare da wani rauni ba, an dakatar da amfani da jiragen kamfanin Max Air na tsawon wata uku.
Hukumar binciken hadurran jiragen sama ta Najeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin, rahoton Channels tv.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, hukumar NCAA ta bayyana cewa za ta ba da duk goyon bayan da ake bukata ga NSIB domin gudanar da bincike mai zurfi.
Dalilin dakatar da kamfanin Max Air
Daraktan hulɗa da jama’a da kare hakkin fasinjoji, Michael Achimugu, ya bayyana a wata sanarwa cewa:
"Ba zamu iya faɗin maƙasudin hatsarin ba har sai bayan NSIB ta kammala bincike. Tuni NCAA ta riga ta fara nazari kan haɗarin dukkan kamfanonin jirage ciki har da Max Air kuma an kusa kammalawa."
"Amma saboda abin da ya faru, kamfanin Max Air zai dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragensa a cikin gida na tsawon watanni uku daga karfe 12 na daren 31 ga Janairu, 2025.
"Hakan zai bai wa kamfanin damar gudanar da cikakken bincike kan ayyukansa."
Gwamnati za ta binciki kamfanin Max Air
Achimugu ya bayyana cewa a cikin wadannan watanni uku, NCAA za ta gudanar da cikakken bincike kan lafiyar kamfanin Max Air a bangaren tsaro da tattalin arziki.
"Binciken tsaro zai kunshi duba yadda kamfanin ke tafiyar da harkokinsa, hanyoyin aikinsa, ma’aikata da jiragensa kamar yadda sashe na 1.3.3.3(b) na dokokin sufurin jiragen sama na Najeriya ya tanada.
"Haka nan za a yi duba na musamman kan karfin tattalin arzikin Max Air don tabbatar da cewa kamfanin na da karfin arzikin ci gaba da harkokinsa.
"Ayyukan Max Air na jigilar fasinjoji a cikin gida za su dawo ne kawai idan kamfanin ya cika dukkan sharuddan da binciken zai gindaya," in ji shi.

Kara karanta wannan
Jirgin Max Air da ya tashi daga Legas zuwa Kano ya yi hatsari, an samu karin bayani
Jirgin Max Air ya yi haɗari a Kano
Tun farko kun ji cewa wani jirgin saman Max Air da ya ɗauko fasinjoji daga jihar Legas ya gamu da tangarɗa a lokacin sauka a Kano.
Wani fasinja ya tabbatar da faruwar hadarin, inda ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin tashi da saukar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng