Hankulan jama'a sun tashi yayinda tayan jirgi ya fashe da fasinjoji cike a Abuja

Hankulan jama'a sun tashi yayinda tayan jirgi ya fashe da fasinjoji cike a Abuja

Hankalin fasinjoji a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja ya tashi da yammacin ranan Lahadi yayinda tayar wata jirgin kamfanin Air Peace ta fashe yayinda take cikin gudu tanan kokarin tashi.

An tattaro cewa fasinjojin dake cikin jirgin wadanda suka nufi jihar Edo da Abuja sun ga tashin hankali yayinda direban jirgin ya rude yana kokarin gudanar da jirgin bayan fashewar tayar.

Hankulan jama'a sun tashi yayinda tayan jirgi ya fashe da fasinjoji cike a Abuja

Hankulan jama'a sun tashi yayinda tayan jirgi ya fashe da fasinjoji cike a Abuja
Source: UGC

Wani fasinja mai suna Johnson yace: "Jirgin ya fara gudu ne a filin jirgin saman yana kokarin tashi kawai sai daya daga cikin tayoyin ya fashe. Wannan ya tayar da hankulan fasinjojin amma direban jirgin kwararre ne sosai tunda har ya iya tsayar da jirgin."

Wata majiya tace: "Wannan abu ya faru ne misalin karfe 5:40 na yamma kuma jirgin kamfanin Air Peace ce. An shawo kan al'amarin inda aka janye jirgin daga jan hanya kuma fasinjojin suka. Ana kan gyaran jirgin a yanzu."

Mai magana da yawun kamfanin jirgin Air Peace, Chris Iwarah, ya tabbatar da wannan labari ga manema labarai inda ya ce an tura injinoyoyin kamfanin su duba abinda ya faruda jirgin.

Allah dai ya kiyaye wani hadarin jirgi saboda a kwanakin kusa-kusan nan, cikin fasinjojin jirgin sama da dori ruwa bisa ga rashin kyakkyawan kula da ke sabbaba wasu matsaloli a jiragen sama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel