An Kama Mai Safarar Makamai ga 'Yan Bindiga daga Nijar zuwa Najeriya

An Kama Mai Safarar Makamai ga 'Yan Bindiga daga Nijar zuwa Najeriya

  • Dakarun sojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami'an farin kaya na DSS sun yi nasarar kama kayan yaƙi da ake shirin shigarwa jihar Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaron sun cafke wani da ake zargi da safarar makaman daga Nijar domin kawo wa 'yan bindiga a yankin Arewa
  • Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya ce hare-haren ‘yan bindiga na raguwa a jihar sakamakon matakin da gwamnati da jami'an tsaro ke dauka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya jinjinawa Hukumar Tsaro ta DSS bisa nasarar cafke wani mai safarar makamai da kayayyakin yaƙi da ake shirin shigarwa jihar.

A ranar Talata, daraktan hukumar DSS a Zamfara ya nuna wa gwamnan makaman da aka kama a fadar gwamnati da ke Gusau.

Kara karanta wannan

An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Makamai
An kama mai safarar makamai daga Nijar zuwa Najeriya. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama makamai a Zamfara

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa makaman da aka kama sun haɗa da:

- Bindiga kirar RPG guda ɗaya

- Bindigogi masu sarrafa kansu guda biyu

- Bindigogi kirar AK47 guda tara

- Bingigogi kirar Pistol guda biyu

- Rumbun harsashi guda 19

Rahoton ya ƙara da cewa wanda ake zargi da safarar makaman ya taso daga jamhuriyar Nijar, inda jami’an DSS suka bi sawunsa har aka cafke shi a hanyar Zurmi/Kauran Namoda.

Gwamna ya yaba wa jami’an tsaro

Yayin duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cigaba da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jihar wajen yaki da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun cafke mai safarar makamai daga Nijar zuwa Najeriya

A cewar gwamnan:

"Dole ne in yaba da ƙwazon dakarunmu, sojoji, ‘yan sanda, musamman jami’an DSS bisa irin wannan gagarumin nasara da suka samu.
"Wannan na nuna irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro a fafutukar da muke yi na kawo ƙarshen ‘yan bindiga a Zamfara."

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro domin ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.

Dauda Lawal: 'An rage 'yan bindiga a Zamfara'

Gwamnan Dauda Lawal ya bayyana cewa harin ‘yan bindiga na ƙara raguwa a jihar sakamakon matakan da hukumomin tsaro ke ɗauka.

"Abin da zai ba mutane sha’awa shi ne, mafi yawan waɗannan ‘yan ta’adda ‘yan asalin Zamfara ne, ba baki ba.
"Kuma ba wannan mutumin kaɗai aka kama ba. A cikin ‘yan makonnin nan an samu ƙarin kama masu aikata irin waɗannan laifuffuka, sai dai ba duka muke bayyanawa ga jama’a ba."

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

- Gwamna Dauda Lawal

A ƙarshe, Gwamna Lawal ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba da goyon baya ga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Zamfara.

An kama mai sata a masallaci a Ogun

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta sanar da kama wani matashi da ake zargi ya sace kayan masallaci a jihar Ogun.

Kakakin 'yan sandar jihar ta bayyana cewa kayan masallacin da aka sace sun kai sama da rabin Naira miliyan 1 kuma za a gurfanar da wanda aka kama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel